Fitacciyar Jarumar Kannywood Umma Shehu ta bayyana cewa zage-zagen da ake yi mata ba du ɗaɗata da kasa ba ballanta na har ta damu.
Umma ta bayyana wa BBC Hausa cewa masu saka mata ido suna aikin banza suke yi domin ta Allah ba ta su.
” Idan mutane za su rika maganata suna yi wa kan su ne domin zunibi na suke kwashewa. Ni bana shirka kuma duk laifin da nayi wa Allah na tsakani na da shi ne zan koma in roke shi gafara. Amma masu zagi na suna kwashe min zunibai.
‘ Uwa ta na da ranta kuma ta na yi min addu’a. Saboda haka can wa sa’idawwa’. Duk masu zagi sun yi ea kansu, ranar kiyama ko dun ki ko sun so za a wafci ladar a bani in yi gaba in bar su a ‘Checkpoint’
Umma Shehu ta ce da ira da Rahama Sadau, an sa musu ido. Daga sun ce cas za a ce musu kule, ko daidai suke ko ba daidai ba sai an samu masu yi musu sharhi.
Umma Shehu na daga cikin fitattun jaruman Kannywood mata da suka yi fice.