Kotun gargajiya dake Mapo a Ibadan ta raba auren shekara 12 tsakanin Oluwaniyi Olajire da matarsa Omolabake saboda Olajire na zargin matarsa da bin mazaje a waje da kuma saka kayan dake nuna surarta.
Alkalin kotun Mrs S.M. Akintayo ta ce ta raba auren ne domin a samu zaman lafiya tsakanin Olajire da Omolabake.
Alkalin ta yanke hukuncin bai wa Omolabake ikon kula da ‘yayan su uku.
Ta Kuma ce Olajire zai rika biyan Omolabake naira 15,000 kudin ciyar da ‘yayan sannan da shi da mahaifiyar yaran za su rika karokaro suna biyan kudin makarantan ya;yan nasu.
“Yaran na da yancin zuwa yin hutu tare da mahaifinsu a duk lokacin da suka samu hutu a makaranta.
Akintayo ta gargaddi Omolabake da ta nisanta kanta daga gidan Olajire sannan ko kadan kada ta ci zarafinsu ta kowace hanya.
A kotun Olajire wanda ke zama a Koro-Akobo a Ibadan ya bayyana cewa Omolabake ta zama karya wajen neman maza.
“Tun farko auren Omolabake da na yi a shekaran 2010 ban san cewa kuskure.
“Tun bayan da muka yi aure Omolabake ta rika kwana da mazaje har tana kwana da su a cikin gidana.
“Omolabake kan yi shiga irin wadan bai kamaci matan aure ba sai da dama na Kai Kara ta wajen iyayen ta amma ta ki bari.
A jawabinta ta ta ce gidan giya ta ke da shi. ” Dole maza su rika muamula da ni aki akai.