Sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Inuwa ya bayyana cewa ba shi da wata alaƙa da ƴan bindiga kamar yadda ake ta raɗe-raɗin cewa wai yana da alakar kud da kud da ƴan bindiga a jihar, yace shima ya ɗanɗana azabar su kamar sauran mutane.
Inuwa wanda aka nada sakataren gwamnatin Katsina tun bayan zaman Aminu Masari gwamna ya bayyana aniyarsa na yin takarar gwamnan jihar a 2023.
Mutane da dama na zargin Inuwa da hada hannu da ‘yan bindiga da hakan ya sa matasa suka kona gidan sa dake karamar hukumar Danmusa a shekarar 2019.
Danmusa na daga cikin kananan hukumomin jihar Katsina da suka fi fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Ni ma na yi fama da hare-haren ‘yan bindiga
Yayin da yake ganawa da manema labarai ranar Laraba a lokacin da yake bayyana aniyar sa ta yin takarar gwamnan jihar Inuwa ya ba shi da alaka da ƴan bindiga fomin shima yayi fama da azabar da suka rika gallaza wa mutane, bai kubuta ba.
Ya ce sau biyu yana sadaukar da ransa wa domin a samu daidaituwa tsakanin gwamnati da ƴan bindiga kawai domin a samu zaman lafiya a jihar.
“A kan babur na yi dogon tafiya cikin gungurmin daji domin kawai a samu zaman lafiya. Na yadda suka yi garkuwa da ni domin shugaban su ya je ya tattauna da gwamnati
“Na yi haka ne domin a samu zaman lafiya a jihar kuma saboda na yadda da gwamna da kokarin da gwamnati ke yi don kawo ƙarshen hareharen ƴan bindiga a jihar.
“Ko su ‘yan bindigan sai da suka yi mamakin gani a wannan lokacin.
Da yake bayanin yadda ya yi fama da hare-haren ‘yan bindiga Inuwa ya ce ‘yan bindiga sun yi garkuwa da babban Wansa, ‘yar dan uwansa da abokinsa a Danmusa da dole sai da suka biya kudin fansa kafin aka sake su.
“Mukan zauna da ƴqn bindigan da suka tuba sduk bayan sati biyu domin tattaunawa da yadda za mu sassanta da sauran ‘yan bindigan.
“Sannan lokacin da maganan sassantawa da gwamnati ya rushe wasu daga cikin tubabbun ‘yan bindigan sun koma ruwa suna kai wa mutane hari.