Dakataccen Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Abba Kyari, ya zargi jami’an NDLEA da haɗa baki da dillalan muggan kwayoyi ana safarar ƙwayoyin cikin Najeriya.
Abba Kyari wanda NDLEA ta gurfanar a kotu bisa zargin hannun sa cikin safarar hodar ibilis, ya ce jami’an NDLEA sun yi gina masa rami ne ya faɗa, su ka yi masa sharrin cewa ya na mu’amala da hodar ibilis.
Babban laifin Abba a wurin NDLEA, a cewar sa, don kawai ya nemi hukumar ta biya wani ɗan kwarmato haƙƙin sa, bayan ya taimaki Jami’an Tsaron Ɗaukin Gaggawa sun kama wani da ake zargi na safarar muggan ƙwayoyi.
‘Jami’an NDLEA Dillalan Muggan Ƙwayoyi Ne’ -Abba Kyari:
Cikin wata takarda a Abba Kyari ya damƙa wa kotu ta hannun wani mai suna Muhammad Nur Usman, ya bayyana cewa shi ƙanin Kyari ne, ya shaida wa kotun cewa akasari dayya NDLEA ke haɗa baki da masu safarar ƙwaya, ita ce yadda idan sun shigo da ita, ake barin su wuce ba tare da an yi masa bincike ba.
Muhammad Nur ya ce idan ma ta kama, wasu lokutan har rakiya jami’an NDLEA ke yi wa dillalan ƙwayar”. Haka dai jaridar Vanguard ta ruwaito.
Da ya ke ci gaba da ƙara bayar da bayanin yadda ya tsinci kan sa a hannun jami’an NDLEA, Kyari ya ce, “A ranar da abin ya faru, waɗanda su ka shigo da hodar ibilis ɗin daga Habasha zuwa filin jirgin saman Enugu sun dira filin jirgin.
“Sai jami’in NDLEA ya ƙyale shi ya wuce, ba tare da bincike ba, domin dama sun san ya na tafe, kuma sun san abin da ya shigo da shi. Daga nan sai jami’an FIB-IRT suka kama shi, ta hanyar kwarmata masu da wani mai kwarmato ya yi.
“Dama kuma kafin mai kwarmaton ya yi aiki da FIB-IRT ɗin, sai da aka yi yarjejeniyar cewa za a biya shi ladar sa.
“Ganin yadda jami’an NDLEA ne da kan su aka haɗa baki su ka ƙyale mai safarar ya fita daga filin jirgi da hodar ibilis ɗin, kai su ka tafi da shi ofishin NDLEA su ka kuma kai ƙarar su a can.
“Maimakon manyan jami’an NDLEA su yi abin da ya dace, su hukunta jami’an su, sai su ka riƙa ƙoƙarin danne maganar, har suka fusatar da mai kwarmaton yayin da ya ke ta ƙoƙarin bin haƙƙin ladar kwarmaton sa.
Yadda Abba Kyari Ya Shigo Batun Kama Hodar Ibilis -Inji Ƙanen Sa:
Ganin yadda aka hana mai kwarmato haƙƙin sa, to sai Abba Kyari ya shiga maganar, ganin cewa babban jami’in NDLEA wanda ke ƙoƙarin hana haƙƙin, abokin Abba Kyari ne.
“To jami’in NDLEA ɗin da ya ƙi biyan mai kwarmato haƙƙin sa, shi ne ya shirya wa Kyari sharri da gadar-zare, su ka ce wai ya na ƙoƙarin ya ba su cin hanci. Kuma babu wata ƙwaƙƙwarar shaida.
“Daga nan kuma Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta kama Kyari s ranar 12 Ga Fabrairu, 2022, saboda kawai an rubuta ƙorafi na ƙarya da sharri a kan sa, aka damƙa shi ga NDLEA.”
Har yanzu dai ana ta ƙoƙarin karɓar belin Kyari, duk da Mai Shari’a ya hana, za a sake nema a zaman kotu na gaba.
Discussion about this post