Wani magidanci mai suna John Anya ya kai karar matarsa kotu dake Igando jihar Legas yana rokon kotu ta raba auren wanda ya kai shekaru 33 saboda tsanananin rashin zaman lafiya.
A rokon da ya yi Anya wanda dankwangila ne kuma mazaunin layi na 7, Unity Avenue, Akesan, ya ce matarsa na lakada masa dukan tsiya sannan gashi bata iya sana’ar komai ba.
Ya ce Egobeke kan ci masa mutunci a duk lokacin da ta ga bashi da kudi.
“Na yi kokarin bude mata sana’ar da za ta rika yi amma bayan kwana biyu sai ta lakume jarin da dawo gida ta yi min zugum, sannan ba daman in yi mata magana, sai ta hauni da masifa ta rika sirfa ta kamar ta samu gero.
“Akwai ranar da Egobeke ta shake ni a wuya, ba dun Allah ya sa ina da sauran kwanaki a gaba ba da tuni na bakunci lahira.
“Har gudu nake yi daga gidana koma can cikin cocin mu saboda tsoron duka da rashin mutuncin da wannan mata tawa ke gurza min.
” Ya’yan mu biyar tare amma saboda rashin mutuncin da uwarsu ke gurza min, su kansu basu ganina da mutunci. Wannan shine dalilan da ya sa naji gaba daya ta fita min a rai kuma na hakura da auren kowa ya kama gaban sa kawai.
Ita Egobeke ta karyata duk abin da Anya ya fadi a kanta a kotu tana mai cewa bata so a raba auren.
Egobeke ta ce mijinta baya bata isasshen kudin cefane sannan kullum cikin kila ta ke tashi haka kuma take kwana.
” Sannan kuma ga dan banzan neman mata, har kawaye na bai barsu ba. ya kan zaga ya su sadu akai akai.
“Ya ce ni ce nake lakada masa dukan amma a dubu jikinsa babu rauni ko tabo ko daya a jikinsa amma akwai a nawa jikin.
Alkalin kotun Koledoye Adeniyi bayan ya saurari ma’auratan ya dage shari’ar zuwa ranar 31 ga Maris.