Rikici ya taso a Cibiyar Bincike da Bunƙasa Masana’antu ta Ƙasa (FIIRO) da ke Oshodi, Legas, bayan an ƙara wa tsohon Darakta Janar na cibiyar girma zuwa Shugaban Sashe, lamarin da ya kauce wa shawarwarin kwamitin binciken da Shugaban Ma’aikatan Gwamnantin Tarayya ya kafa.
Kwamitin dai ya kama tsohon Babban Daraktan da laifi, kuma ya bayar da shawarar a yi masa dafkal, a maida shi Babban Mai Bincike.
Sai dai kuma a yanzu an maida shi shugaban ɓangare kamar yadda wata wasiƙa ta nuna, wacce ke ɗauke da umarnin ƙara masa girman.
An ƙara wa Dakta Chima C. Igwe girman ba a kan ƙa’ida ba, sannan kuma an yi hakan a lokacin da ya ke fuskantar tuhuma a Kotun Shari’ar Laifuka na Musamman da ke Ikeja, Legas, wadda Hukumar ICPC ta gurfanar da shi.
A wannan Kotun Musamman dai ana tuhumar Igwe da yin fojare, amma har yanzu bai amsa laifin sa ba, tun cikin Nuwamba, 2021 da aka gurfanar da shi.
Tuni dai Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Asibitocin Koyarwa, Cibiyoyin Bincike da Manyan Hukumomi (SSAUTHRAI), su ka yi tir da wannan ƙarin girma da aka yi masa, wanda su ka bayyana da cewa, “hali ne na nuna ƙarfa-ƙarfa da yin yadda aka ga dama, wanda wasu manyan jami’an cikin gwamnati ke aikatawa.”
Shugaban ƙungiyar Mumeen Togunde ya ce bai kamata a bar wasu ‘yan baragada su na kawo harmagaza a lokacin da ake ƙoƙarin tsaftace cibiyar binciken ba.
Togunde ya ce dama tun da aka rage wa Igwe muƙami bai sake zuwa ofis ba, “amma a kullum ya na ofishin Minista ya na kamun-ƙafar neman a maida shi kan muƙamin sa.”
“Amma zan tabbatar maku cewa ba za mu bari wannan rashin kunyar da rashin mutunci su ɗore ba. Mu ne fa mu ka yi jidalin fallasa badaƙalar da aka yi, don haka ba za mu kwanta mu na barci ba, ganin yanzu maganar ta na kotu har sai mun ga ƙwal uwar daka.” Inji shi.
Ya ci gaba da cewa bai sani ba ko ya maida wa cibiyar kuɗaɗen da aka kama shi ya danne.
Sai dai kuma Shugaban Cibiyar Bincike da Bunƙasa Masana’antu ta Ƙasa, Magaji Gambo, ya shaida wa wakilin mu cewa ba zai yi magana da shi ba.
Shi ma Shugaban Riƙo na Hukumar ya ce ba zai yi magana ba.
Premium Times ta ga takardar da aka bayar da umarnin ƙara masa girma, wadda aka rubuta a ranar 21 Ga Maris, 2022 mai ɗauke da sa hannun Daraktan Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha, C.A Ibe.
A cikin takardar an rubuta cewa Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu ya amince da ƙarin da aka yi ɗin.
Discussion about this post