Sanadiyyar tashin hankali da barke a wasu sassan kananan hukumomin Jema’a da Kaura, gwamnatin jihar Kaduna ta saka dokar hana walwala na awa 24 a faɗin kananan hukumomin.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya sanar da haka a takarda da ya fitar ranar Litinin a garin Kaduna.
Aruwan ya ce an saka wannan doka ce domin jami’an tsaro su iya shawo kan tashin hankalin da ya ɓarke a tsakanin mutanen kananan hukumomin kafin ya yaɗu zuwa wasu sassan yankunan dake karkashin kananan hukumomin.
Ya ce da zarar an samu natsuwa da kwanciyan hankali gwamnati za ta sanar da inda aka do sa.
Yayi kira ga mutanen jihar da su kwantar da hankalin su gwamnati da jami’an tsaro na aiki tukuru domin kawo karshen matsalolin rashin tsaro a jihar
Discussion about this post