Wani mai suna Gbenga Adewoyin ya ƙalubalanci bokaye da masu yi wa mutane rufa ido da su fito a gaban sa su maida mutum mage ko kuma doya kiri kiri ana gani, shi kuma zai baiwa duk wanda yayi haka kyautar naira miliyan 2.5 nan take.
Wannan rahoto me da shafin BBC ta turanci ta buga inda ta nuno wannan mutum a cikin kasuwanni a jihar Ogun da Oyo yana neman irin waɗannan bokaye su tabbatar masa da wannan abu.
Bokanci yayi suna sannan ya samu gindin zama a musamman yankin kasashen Afrika.
Mutane da dama sukan yarda da al’amarin bokaye ta hanyar kai musu ziyara akai akai suna neman su samu arziki, ko kuma karfin iya canja wani abu zuwa yadda suke.
Malaman addinai Kiristoci da Musulmai da dama sukan faɗa cikin irin wannan kamayamaya.
Sai dai kuma Adewoyin na ganin abin rufa ido ne kawai babu gaskiya a cikin sa. Ya fito karara yana bin garuruwa musamman kasuwanni ya na neman wanda zai ya ke ganin idan zai iya maida kansa mage nan take ko kuma ya iya maida mutum doya ya bayyana a gaban sa idan da gaskene ya zama doya shi kuma zai mika masa naira miliyan 2.5 nan take.
A ganin Adewoyin, irin waɗannan siddabaru da yaudara da ake yi wa mutane ya sa ake samun kashe kashe a kasar nan na babu gaira babu dalili wai don ayi kudi, wato arziki.
Wani ɗan kasuwa ya ce ” wannan bai san abinda yake yi bane. Tabbas akwai tsafi da asiri, nima ga nawa nan. ( Ya ciro wasu bakaken layu ya nuna wa Adewoyin) na kariya fa buɗi ne.” Sai dai kuma da aka ce ya fito ya nuna irin abin da layun na sa suke yi ya caske naira miliyan 2 da rabi, sai ya ki.
Wani malami. Jami’a dake karantar wa a jami’ar Ibadan Dr Olaleye Kayode, ya tabbatar cewa lallai irin wannan tsafi da ake haɗa wasu sassan ɗan Adam a yi wa mutum kuɗi hakika gaskiya ne. Wato a haɗa asirin mutum ya wayi gari ya ga shirgegen kwalla cike makil da kudi.
Ya ce waɗannan kuɗade da ake gani sabbi cike a cikin kwalla, daga banki ake samo su. Inji Dr Kayode.
” A nawa ganin da irin wannan kuɗi da gaske ana yin su, da kuɗi ya cika kasa ana ta hada hada, sannan tuni da an samu karayar tattalin arziki wato ‘Infilation’.
Adewoyin ya ƙalubalanci duk wani da ke ce wa wai shi kaifin wuka ko reza bata huda shi ya bayyana a gaban sa ya gwada idan lallai bata huda shi ba zai caske masa naira miliyan 2.5 nan take.
Shi ko ministan yaɗa labarai Lai Mohammed cewa yayi an samu matsalar karkata ga harkokin bokaye ne kamar yadda wasu finafinan da ake yi ke tallata haka. Ya ce masu kallo da yawa kan ga kamar abinda ke faruwa gaskiya ne mutum ua rikiɗa ya zama mage ko kuma kawai haka nan sai a wayi gari kuɗi masu yawa su bayyana him a gidan ka.
Sai dai kuma Kanayo O Kanayo mai shirya finafinai na Nollywood ya ce kada a dora wa farfajiyar Nollywood laifi. Shima sana’ar su da ban abind mutane ke yi a waje da bam.
To ga dai fili ga doki nan, ana kalubalantar wanda ya iya zama mage ko ya canja mutum ya koma doya ya zo ya nuna kwarewar tsubbun sa ya caske naira miliyan 2.5.
Wannan rahoto ne da BBC turanci ta buga wanda Nduka Orjinmo ya rubuta.
Discussion about this post