Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa ta bazama wajen bayar da fifikon gina ayyukan raya ƙasa ne a faɗin Najeriya, domin sauƙaƙe wa jama’a ƙuncin rayuwar da su ke ciki.
Buhari ya yi wannan bayanin a ranar Talata a Abuja, lokacin da ya karɓi baƙuncin wata tawagar da ta kai masa ziyara daga Jihar Kaduna, a ƙarƙashin jagorancin Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli da kuma Mataimakiyar Gwamnan Kaduna, Hadiza Balarabe.
Ya ce tunda aka kammala aikin titin mota da na jirgin ƙasa daga Legas zuwa Ibadan, lamarin zirga-zirga ya bunƙasa sosai.
“Ni dama manufofi na a bayyane su ke, duk da ƙarancin kuɗaɗen shigar da Najeriya ke samu, na sha alwashin magance matsalar rashin gina ayyukan inganta ƙasa da ba a kula da su can a baya ba.
“Idan muka dubi tarihin yadda ƙasashe suka ci gaba, su ka bunƙasa a duniya, za mu ga kowace a cikin su sai da ta inganta ayyukan raya ƙasa sannan ya haye matakin ci gaba.
“A da muna da titinan jiragen ƙasa. Mutanen kudancin Kaduna za su iya tuna wannan.
“Wace ƙasa ce za ta iya ci gaba ba tare da ta inganta titinan ta ba na motoci da titinan jiragen ƙasa da wutar lantarki? Dalili kenan na yi tunanin gara na magance matsalar kayan inganta ƙasa.
“Na san ‘yan Najeriya akwai don gasar rige-rigen harkokin kasuwanci. To idan aka gyara titinan motoci, na jiragen ƙasa da makamashi kuwa, harkokin kasuwancin ƙaruwar zai yi sosai.” Inji Buhari.
Buhari ya tabbatar masu da cewa za a ci gaba da samar da ayyukan raya ƙasa, ciki har da aikin ginin tagwayen titinan Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano, wanda kamfanin Julius Berger ke kan aikin ginawa.
Buhari ya kuma yaba da irin ayyukan raya ƙasa da Gwamna Nasir El-Rufai ya ya yi da waɗanda ya ke kan yi a jihar Kaduna.
Mataimakiyar Gwamnan Kaduna, Hadiza Balarabe da Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli sun yi jawaban godiya.
Discussion about this post