Tsohon Ministan Wasanni na gwamnatin Buhari tsakanin 2015 zuwa 2019, ya yi wa jam’iyyar su ta APC tir, saboda kasa cika wa ‘yan Najeriya alƙawurran da ta ɗaukar masu kafin a zabe ta.
Dalung ya yi wannan kakkausan sukar a wurin taron ƙaddamar da wata jam’iyya mai suna “The National Movement”, a Abuja ranar Talata.
An yi tunanin ƙirƙirar ƙungiyar tun a cikin 2021, domin zama wani dakalin baza shimfiɗar zaman majalisin ceto Najeriya, daga “halin rashin iya magance matsalolin ƙasar nan da ake fama da shi a ƙarƙashin mulkin APC.”
Duk da Solomon Dalung ɗan jam’iyyar APC ne, amma maganganun sa ya nuna ɓacin rai kan abin da ya kira kasa taɓuka ƙoƙarin ceto ƙasar nan da Gwamnatin Buhari ta yi.
“Na yi ƙaurin suna wajen caccakar gwamnatin Jonathan tun daga 2009 har zuwa 2015. Saboda ni ne mutum na farko da ya fara ragargazar Jonathan lokacin da aka karya doka aka naɗa Jonathan Muƙaddashin Shugaban Ƙasa.
“APC ta same ni ina adawa da gwamnatin Jonathan. To amma a yanzu tilas mu fito mu nemi afuwar jama’a dangane da halin ƙuncin rayuwar da aka jefa su. Saboda lokacin da muka ce za a yi gyara, ba mu yi wa mutane alƙawarin za mu maida buhun shinkafa naira 35,000 saɓanin naira 7,000 da ya ke lokacin da muka karɓi mulki ba.” Inji Dalung.
Solomon Dalung ys bai wa ‘yan Najeriya haƙurin yadda ya riƙa yin kamfen har ya ja hankalin su aka zaɓi APC, amma kuma yanzu ta kasa cika masu alƙawarin da ta ɗauka, shekaru bakwai bayan hawan ta mulki.
“Saboda mun kasa yin ayyukan alƙawurran da mu ka ɗauka, ya sa a matsayi na na Kirista wanda ke da kuma da mutunci, na ga cewa ya zama wajibi na nemi afuwa daga ‘yan Najeriya. Saboda bayan wannan duniyar, akwai da hisabi a kiyama. A can za a tambaye ni, ‘kai Dalung da kai aka riƙa yin kamfen har wannan gwamnatin ta ci zaɓe. Kuma kun yi masu alƙawurra.
“Shin lokacin da ‘yan bindiga ke kashe mutane su na yi wa mata fyaɗe ka fito ka yi magana?”
“Saboda don ina cikin APC ba zan iya yin shiru ba. Duk wani wanda ya yi kamfen wajibin sa ne ya fito ya ba ‘yan Najeriya haƙuri. Ni dai na tuba, ina neman afuwa.” Inji Dalung.
Shugaban taron na ceto Najeriya, tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Kwankwaso, ya ce akwai buƙatar a daidaita ƙasar nan domin a raba ta daga hannun waɗanda banda buƙatar cin zaɓe, babu wani abin da ke gaban su.
Ya nuna damuwa dangane da mummunan halin kashe-kashe da ƙasar nan ke ciki, inda ya ce akwai buƙatar a tashi a haɗa kai a ceto ƙasar nan, domin Najeriya na gaba da muradin duk wani ɗan siyasa.
Discussion about this post