A ranar Asabar ne mazaunan kauyen Nahuche dake jihar Zamfara suka yi tattaki zuwa fadar gwamnati dake Gusau domin mika kukan su ga gwamnatin jihar, su kawo wa kauyen dauki saboda tsananin hareharen ‘yan bindiga da yaki ci yaki cinyewa a yankin.
Mazaunan kauyen sun ce suna rokon gwamnati ta dube su da idon rahama ta ceto mutum 13 dake hannun ‘yan bindiga har yanzu.
Jagoran masu zanga-zangar kuma tsohon shugaban karamar hukumar Bungudu Musa Abdullahi ya ce ‘yan bindiga na yawan kawo wa kauyen Nahuche hari inda bayan mutum 13 da aka yi garkuwa da su kauyen ta rasa rayukan mutum sama da 50 sannan da akalla naira miliyan 200 wajen biyan kudin fansar mutanen da aka yi garkuwa da su da biyan kungiyar ‘yan sa kai.
Abdullahi ya ce da farko an biya Naira miliyan biyar akan mutum uku din da ‘yan bindiga suka fara yin garkuwa da su daga kauyen amma maharan suka ki sakin mutanen domin wai ba a hado da babura biyu ba.
“Kafin mu basu babura biyu ne maharan suka sake yin awon gaba da mutum takwas kuma duk daga wannan kauye na mu.
Kauyen Nahuche kauye ne da duka-duka ba a wuce yawan mutane 300,000 dake zama a cikin sa ba. Amma saboda yawan hare-haren ‘yan bindiga gab muke da kowa ma ya tattara ya fice daga kauyen ya zamo babu kowa kuma.
“Muna kira ga gwamnati da ta aiko mama da sojoji domin samar mana da tsaro a kauyen.
A taron tunawa da sojojin da suka rasa rayukansu a wajen daga na shekarar 2022 da aka yi ranar Asabar gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya ce gwamnati ta ceto mutum 1,800 daga hannun ‘yan bindiga a jihar.
Discussion about this post