Rundunar Ƴan sandan jihar Neja ta bayyana cewa ƴan bindiga sun kashe mutum 13 a karamar hukumar Shiroro.
Kakakin rundunar Wasiu Abiodun ya bayyana haka yana mai karyata rahotanni da aka rika yaɗawa a kafafen labarai wai mutum 32 ƴan bindigan suka kashe.
Abiodun ya ce ƴan bindigan sun afka wa wasu manoma ne a gonakin su suna aikin a ranar Talatan makon jiya.
Bayan haka kuma gwamnan jihar Sannan Abubakar Bello ya bayyana cewa wasu ƴan bindigan sun afka wa mutane a kauyen Wurukuchi duk a wannan hare-hare da suka kai
Mai taimaka wa gwamnan jihar kan harkokin yaɗa labarai Mary Noel-Berje ta ce gwamna Bello ya yi alhinin abin da ya faru a waɗannan garuruwa sannan ya yi alkawarin gwamnati za ata kawo karshen wannan ta’addancin da mutane ke fama da shi a jihar.
A ranar Lahadi rundunar ta sanar da yin garkuwa da wasu mutane 15 a kauyen Kulhu dahlke karamar hukumar Mashegu.
Abiodun yace maharan sun afka kauyen Kulhu ne da misalin karfe biyun dare suka kwashe mutane 15.” kuma sun kwashi dabbobi masu yawa wanda har yanzu ba a iya tantance yawan su ba.
Sakamakon wani bincike da aka yi ya nuna cewa a cikin shekara biyu ‘yan bindiga sun raba akalla mutum 151,380 da matsugunan su wanda mafi yawan su manoma ne a jihar Neja.
Discussion about this post