Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta damƙe wani magidanci mai suna Ali Lawan da ake zargi da cin zarafin ƴarsa mai shekara 3 a karamar hukumar Kirfi.
Kakakin rundunar Ahmed Wakil ya ce kama Lawan na daga cikin kokarin da rundunar ke yi na ganin an kawo karshen ireiren haka a jihar.
“A ranar 9 ga watan Janairun 2022 mahaifiyar wannan yarinyar Maryam Abdullahi ta sanar wa ƴan sanda cewa mijjnta Ali Llawan ya umarceta ta mika masa tabarma ya shinfidar da ‘yarsu da ke yi barci a jikin sa.
“Maryam ta ce sai dai daga baya bayan ta mika masa tabarmar ta yi tafiyar ta da ta sai ta iske ‘yarta na amai ta baki da hanci sannan gabanta ya kumbura.
“Zuwa yanzu likitoci na duba yarinyar a asibiti amma kuma sakamakon gwajin da aka ya ya tabbatar da an ci zarafin wannan baiwar Allah. Amma dai za a ci gaba da bincike sannan za akai mahaifin kotu nan ba da dadewa ba.
Bayan haka Wakil ya ce rundunar ta kama wani Adamu Musa mai shekara 27 wanda ya shahara wajen yin garkuwa da mutane a Sabon Garin Batal dake karamar hukumar Tafawa Balewa.
Sannan kuma da wani shima mai suna Ya’u Haruna mai shekaru 25 da bindiga ‘Revolver’ guda daya da harsashi.
Rundunar ƴan sandan jihar ta hori mutane su rika gaggauta tuntubar jami’an tsaro a duk lokacin da suke da bayanan da zai taimaka wajen kama bata gari a jihar.