Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa hadiman Shugaba Muhammadu Buhari ai mutane ne kamar sauran mutane. Don haka ba wani abin mamaki ba ne don wasun su sun kamu da cutar korona.
Femi Adesina ya ce, “dukkan hadiman Shugaban Ƙasa Buhari da suka kamu da cutar korona, sun killace kan su a gidajen su.”
Haka Femi Adesina ya bayyana a tattaunawar sa da gidan talbijin na Channels.
A ranar Asabar Premium Times ta buga labarin cewa wasu hadiman Buhari da ke aiki a Fadar Shugaban Ƙasa sun kamu da cutar korona.
Waɗanda su ka kamu ɗin dai sai fadar shugaban ƙasa ɗin ta yi shiru da bakin ta, ba ta sanar ba.
Har sai bayan labarin ya fita a kafafen yaɗa labarai sannan Fadar Gwamnatin Tarayya ta sanar.
Majiya ta bayyana har da sunan Lai Mohammed Ministan Yaɗa Labarai a cikin waɗanda su ka kamu.
Sai dai kuma daga baya Lai ya shaida wa Premium Times cewa shi korona ba ta kama shi ba, kuma ba ta kwantar da shi ba.
Sai dai Garba Shehu ya tabbatar da cewa ya ɗan kamu, kuma ya killace kan sa.”
Ya ce a yanzu haka har ma ya kusan kammala kwanakin killace kan sa da ya yi, amma ba shi da hujjar ko har yanzu akwai sauran cutar a jikin sa ko babu.
“Ba ni da haƙiƙanin sanin halin da zan ce na ke tukunna. Amma dai na ɗan kamu da korona kaɗan. Kuma Ni dai garau na ke jin kai na. A sani na an yi min alluran rigakafin korona guda ukun da ake yi. Yanzu haka ma na gama ɗan gudun motsa jikin da na saba yi a kullum.
“Ka san wani abin ɗaure kai dangane da wannan cutar, masana kimiyya ne za su auna ka su ce babu sauran ta a jikin ka, ko kuma akwai.
“Yanzu dai na killace kai na. Kuma zan koma domin a tabbatar ko ta fita daga jiki na ko akwai saura. Na gode da kuma tuntuɓe ni.”
Femi Adesina kuwa cewa ya yi “Hadiman Shugaban Ƙasa ba wasu irin mutane ba ne daban. Ba wani abin mamaki ba ne don sun kamu da cuta, domin su ma mutane ne kamar kowa. Za su iya yin rashin lafiya da dukkan wasu cututtukan da sauran jama’a za su iya kamuwa.
Discussion about this post