Hotunan bidiyo sun fi kowanne wahalar tantancewa. Ba kamar rubutu ko hotuna ba, ba za’a iya binciken bidiyo ta sanya shi a cikin shafukan da sukan tantance rubutu ko hotuna a ga ko gaskiya ne ko yana daukar hankali ba, akalla a yanzu haka dai babu wannan fasahar. Bugu da kare bidiyoyin bogi yanzu suna da saukin hadawa kuma sun kara zama masu wahalar tantancewa yayin da fasahar ke cigaba da fiskantar sauyi. Dan haka ‘yan jarida da ‘yan kasashen duniya ba ki daya suna da sabon alhakin da ya rataya a wuyansu, na gaggautawa wajen saun bayanai da tantance su dan tabbatar da sahihancin su.
Babu shakka, tantance bidiyo a shafukan soshial mediya ya na da wahala amma ba zai gagara ba tunda akwai wadan ‘yan shawarwari wadanda idan har mutun ya bi su zai iya tantancewa:
1 – Saita hankali da kyau: Na farko dai, idan mutun na shakkan sahihancin abu, zai taimaka wajen yin bincike dangane da bidiyon. Baya ga shakka mutun na bukatar ya yi azama wajen amfani da irin kayayyakin da za su taimaka wajen tabbatar da ko bidiyon gaskiya ne ko karya.
2 – Kafin amfani da kayayyakin, a duba a gani ko akwai abubuwa takamaimai da mutun ke so ya tabbatar ko karyata a bidiyon da ya zagaya yanar gizo nan da nan. Shin akwai abin da daga gani ka san cewa kagawa aka yi? An kai karar shi ne a kafofin yada labarai na gargajiya?
Haka nan kuma a duba ko bayanan da ke cikin bidiyon sukan sauya bisa la’akari da wanda ya tura. Labarin da ke cikin bidiyon ya banbanta da abin da aka fada dangane da shi a wani dandalin na daban? Wata sa’a akan sauya ainihin labaran da suka faru a cikin bidiyon ta yadda za su fadi wani na labarin na daban da ya zo daidai ajandar wasu.
3 – A yi amfani da manhajoji irin su YouTube Dataviewer wanda Amnesty International ta kirkiro ko kuma InVid wanda mutun zai iya saukewa a kan komfuta. YouTube data viewer bidiyoyin YouTube kadai ya ke dauka amma Invid yana barin mutun ya sanya adireshi ko kuma “link” a turance na ko wane irin bidiyo daga shafukan soshiyal mediya daban-daban idan har mutun yana so ya gano mafarin bidiyon. Invid yana kuma iya bayar da mahimman hotuna (key frames) daga cikin bidiyon wanda za’a iya amfani da shi wajen gano ko an taba wallafa bidiyon a baya.
Yawancin bidiyon da sukan sami yaduwa cikin nan da nan a soshiyal mediya an riga an taba wallafa su, kuma suna kan yanar gizo sake tura wa jama’a kawai ake yi. Misali, bidiyon labarin wani hatsarin tankan man da ya faru a kasar Saliyo bayan fashewar tankan da ya afku ranar 5 ga watan Nuwamban bana.
4 – Baya ga Invid, wata hanyar samun mahimman hotuna ko kuma key frames idan aka dauki hoton bidiyon da wayar hannu. Sai a sanya shi cikin manhajan da za ta iya tantance ko an taba wallafa hoton. Manhajojin Tineye da Google na biyu daga cikin wadanda za’a iya amfani da su wajen gudanar da irin wannan binciken na gano ko an taba amfani da hoton a baya.
5 – Wata hanyar tantance sahihancin bidiyo kuma ita ce sauke bidiyon a duba bayanan da ke jikin shi dangane da girman shi, inda aka nada, wanda ya nada da kwanan watan sadda aka nada da sauran su, wato dai cikakken bayanan da ke cikin bidiyon. Yawancin kafofin sadarwa na soshiyal mediya sukan goge irin wadannan bayanan da zarar aka wallafa bidiyon, amma idan har mutun ya sami wadannan bayanan zai iya gano asalin bidiyon.
6 – Ana iya amfani da manhajan geolocation – wanda ke iya gano wajen da aka nadi abu – wajen tantance ko an nadi bidiyon ne a wurin da aka ce an nada. Idan kuma a waje aka nadi bidiyon, ana iya amfani da Google Earth a gano.
7 – Idan har ba yi nasarar samun wani bayani mai amfani da wadannan kayayyakin ba, a gwada amfani da kalmomi na musamman a cikin labarin wajen aiwatar da bincike a kan google ko youtube sa duba kalmomin da ke da dangantaka da bidiyon. Ana iya gano hotuna masu kama da wanda ke bidiyon wadanda kuma za su iya baku alamun da ka iya kai ga amsar abin da ake nema.
Tantance bidiyo na iya daukar lokaci sosai, idan har ba a yi nasarar tantancewa ba a guji sake raba bidiyon da ba’a san mafarin shi ba. A nemi tantancewa ta wurin wani wanda ke kwarewar yin hakan.