A yanzu dai, bai gaza wasu wattanni ba gwamnatin Muhammadu Buhari zata gama wa’adin ta na karshe, lissafi na nunawa cewa sama da shekaru masu yawa, ‘yan Nijeriya basu taba samun kansu cikin rayuwa mai radadi ba, kamar wannan yanayin.
Banda batun kanfon talauchi da kuma yawan karayar tatttalin arzikin da ita kanta gwamnatin take yawan samu, wanda ya hana tattalin arzikin kasar yin tasiri ga tallakawan kasar, sai gashi zaman lafiya ma cikin yanayin da ake ciki yana nema ya gagara, musamman a yankin da Shugaba Buhari ya fi ko ina farin jini, wato arewa maso yamma da maso gabas dama tsakiyar Nijeriya.
Dalilai da dama sun nuna cewa Shugaba Buhari yafi sauran shugabbnnin kasar nan farin jini a wurin talakawa, wanda shine dan takarar da talakawa suka tara masa kudi don neman wannan kujerar, kuma haka ya faru ne bisa kyakkywan zaton kishin kasar sa, jajircewa da kuma tunanin yana dauke da kyawawan manufofin da zasu sharewa talakawan Nijeriya hawayensu, amma da dukkanin alamu an sami sabanin haka, a yau talauci da karayar arziki a tsakanin yan Nijeriya yayi katutu, hadi da rashin tsaron dama ya hana su yin sana’oin da suka dogara da su, irin su noma da kasuwanci a garuruwan su.
Kafin zaben shekara ta 2015, kasancewar Buhari yayi takara kusan sau biyu kafin wannan lokacin, a kwai kyakkyawan zaton za a samu chanji a Nijeriya bayan nasarar APC a 2015.
Gammayyar APC bisa jagoranci Shugaba Buhari, sun kewaya Nijeriya, anyi tarurruka na yan kasa da masana, matasa, mata da ma masu ruwa da tsaki a harkar siyasa a kan matsalolin Nijeriya, musamman tsadar rayuwar da talakawa suke ciki kamar tsadar abinci, mayin fetur, da makamantan su. Rashin tsaro a wannan lokacin da yafi addabar mutanen arewa maso gabashin Nijeriya, ya zamanto dama da makami na Jama’iyar APC wajen yakin neman zaben da ya gabata na 2015. Har ta kai a wasu lokutan manyan APC na shiga ko jagorantar zanga-zanga ta lumana don farkar da gwamniti yanayin tsanani da ‘yan Nijeriya suke ciki.
Shugabancin Jama’iyar APC bisa jagorancin Shugaba Buhari ya kasa cika burin sa a kan miliyoyin talakawan Nijeriya wayanda suka kasance manyan aminai, abokai da masoya na Baba Buhari, dadi da kari ma kasa ta sake shiga cikin rudani ne a kan wannna matsalolin, wanda laluben bakin zaren dinke matsalolin yayi wuyar samowa.
Manyan dalilan gazawar wannan gwamnati wajen samawa talakawan wannan kasa ingantanciyar rayuwa sun hada:
Rashin kykkyawan shiri, jadawali, tsari da kuma zababbun mutane kafin shiga gwamnati daga Shugaba Buhari, don cimma burin gina kyakkyawan tsarin tattalin arziki da rayuwa mai aminci ga talakawa, ya zama rami na farko da wannan gwamnati ta gina wa kanta.
Bayan rantsar da shugaba Buhari a watan mayu na 2015, Shugaba Buhari ya shafe tsawan wattanni kafin ya kafa majalissar sa ta zartarwa da nada ministoci, domin fuskantar alkawuran masu zabe. La’akari da tarin matsalolin Nijeriya da kuma lokacin da ake da shi na shekara hudu kawai, wannan ya taimaka mutuka wajen gina ingantacciyar gwamnati a Nijeriya. Buhari ya cunkushe hukumo min gwamnati da kuma nada ministoci kadan bisa dalili na tattali ba tare da la’akarin yawan al’umar wannan kasa da kuma dinbin bukatun su ba, wanda daga baya akayi kwam baya da sake kara yawan ministoci a zangon sa biyu.
Gwamnatin shugaba Buhari ta gaza samar da kwamati na kwararru akan tattalin arziki, tsayyaye kuma mai karfi da zai na bada shawara akan yadda za a na tafiyar da harkar tattalin arziki na kasa, wanda ya kamata ya kasance mai ikon kansa.
Shugabancin Babban Bankin Nijeriya wato CBN, da amincewar Shugaba Buhari na Governor Godwin Emefele da yaci gaba da jagorancin CBN duk da kasancewar babu wata nasara da aka samu a jagorancin sa, ta fuskar kawo chanjin a harkar tattalin arziki da gudanarwar kudi a Nijeriya, wanda har yau kullun hauhawar firashi a ke samu kuma Naira kullum darajar ta raguwa take.
Tafiya da Godwin Emefele kadai ya nuna rashin kyakkywan tsarin da Shugaba Buhari yake da shi na tafikar da tsarin tattalin arzikin Nijeriya, kawai zai dorane a kan tsarin baya na Shugaba Jonathon duk da sukan da yasha a baya da shi kansa Buharin. Barin Governor Emefele ya nuna cewa Shugaba Buhari bashi da tsarin kwararrun mutanen da zai yi aiki da su don cika burin mulkinsa.
Waiwaye kawai a kan manufofin CBN na harkar kudade, kusan kara karya darajar Naira yake a ko da yaushe, misali karya darajar naira da CBN tayi saboda annobar korona yayi sila cigaba da karya ta a kasuwanni hada hadar kudade, tsarin CBN na kin sayarwa masu Chanji Dollar wato BDC ya kara karya darajar Naira akan Dollar daga 400 zuwa sama da 500 cikin sao i kalilan, a kullum firashin kayyaki karuwa yakeyi, wanda duk wannan talakawa sun fi shiga tasku.
Shirye shiryen gwamnati na kauda talauchi da tallafawa masu manya da kanan nan sana’oi baya aiki dari bisa dari, a wani bangaren ma yana kawai cusa al’umma cikin kaka na kayi ne kawai da kuma barnatar da kudin al’umma, yayin da gwamnatin ta kau da kai akan matsalolin ilimi, da lafiya, wanda kullum likitoti da malamai suna kan haryar yajin aiki.
Tallafin gwamnati na bada bashi irin na Covid 19 da Survival fund, cash transfer, duka suna da kyawawan manufa kamar yadda a kayi bayani, sai dai shin gwamnati tana da cikekken bayanai na wayanda zata bawa bashin da tallafin kafin a raba kudin? Shin wa yanda suka karu da wannan tallafin sune ma ingantattun masu sana’ar? Shin hukumomin gwamnati sun bibiyi yadda wayanda a ka ba kudin yadda suka gudanar da shi, yaya za a karbi wannan kudaden ga wayanda a kaba bashi.
Tsarin shugaba Buhari na hana shigowa da abinci daga makotan kasashe wanda kai tsaye yafi shafar jahohin da ke kan iyaka, wannan tsarin duk da kykkyawar manufar sa, amma dai bai zo da tsarin kata-kwana ba, a kan matsalolin da zasu iya biyo bayan sa ba, musamman na tashin kayan abinci da kuma rashin aikin yi ga al’ummar da suke wannan sana’ar. Wanan ya kawo karanci da tsadar abinci cikin karamin lokaci da kuma kara talauci ga masu wannan sana’ar.
Shin cigaban da ake cewa an samu na arzikin kasa wato GDP baya nunawa ne wajen canja rayuwar talakawan Nijeriya? Tabbas akwai tazara mai yawa tsakanin cikagaban tattalin arzikin da dai-dai kun ‘yan Nijeriya da kuma cigaba hukumomin Nijeriya. Shine ya sanya karuwar talauchi da karayar tattalin arzikin al’umar Nijeriya.
Wannan suna da ga cikin kadan daga dalilan da ya sanya gwamnati kasa cimma burin bunkasa tattalin arzikin yan Nijeria.
alhajilallah@gmail.com