KISAN RUBDUGU: Korona ta ci rayuka 59, ta kama mutum 964 ranar Asabar

0

Yayin da Najeriya ke fama da cutar korona Aji na 3 mai saurin kisa da nuƙurƙusarwa, Hukumar Ɗaƙile Yaɗuwar Cutar Korona (NCDC), ta fitar da ƙididdiga cewa korona ta kashe mutum 49 a ranar Asabar.

Sanarwar ta ƙara da cewa korona ta kuma kama mutum 964 a ranar Asabar ɗin.

Sai dai kuma sanarwar NCDC ta ce yawan waɗanda cutar ta kashe da kuma wadanda su ka kamu ɗin a ranar Asabar, sun yi yawa ne saboda Jihar Lagos ba ta bada ƙididdigar waɗanda su ka mutu ko su ka kamu a ranar Juma’a ba.

NCDC ta ce Legas ta bada adadin masu yawa a ranar Asabar, saboda ba ta bayar a ranar Juma’a ba.

Yawan waɗanda korona ta kashe a ranar Juma’a dai mutum 7 ne, inda hakan na nuni da cewa adadin waɗanda aka bada ƙididdigar mutuwar su har 49 sun yi muni ƙwarai.

Haka ma yawan waɗanda cutar ta kama a ranar Asabar har mutum 964, sun nunka yawan mutanen da su ka kamu a ranar Juma’a, su 456.

A daidai lokacin da ake samun yawan mutuwa dalilin korona, a lokacin kuma jama’a ke ta ƙara gwasale gwamnatin tarayya, tare da ƙaryata cutar.

Da dama kuma cikin waɗanda su ka yarda akwai ta, su na ƙorafin rashin wadatar rigakafin korona.

Masana na ganin har yanzu an bar Afrika a baya wajen rigakafin korona, inda har yau a Afrika ba a yi wa ko kashi 3 bisa 100 na al’umma ta rigakafin korona ba.

Share.

game da Author