Rundunar ƴan Sandan Jihar Neja sun tabbatar da labarin yin garkuwa da Hakimin Wawa da ke cikin Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja.
Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun ya shaida wa manema labarai a ranar Lahadi cewa an arce da hakimin wajen ƙarfe 10 na dare a ranar Azabar.
Sai dai kuma ya ce zaratan ‘yan sanda tare da ‘yan bijilante sun afka daji domin ƙoƙarin ceto hakimin.
Yayin da ya bada tabbacin ganin cewa za su yi bakin ƙoƙarin ganin an ceto hakimin, Abiodun ya kuma roƙi jama’a su riƙa kwarmata wa jami’an tsaro duk inda su ka ji motsin wani mugu da inda duk su ka san mugaye na fakewa.
Jihar Neja na ɗaya daga cikin jihohin da ‘yan bindiga su ka yi wa kakagida.
Ta na daga cikin jihohin da gwamnonin su su ka haramta cin kasuwannin mako-mako a cikin wannan mako.
Discussion about this post