Wasan gasar cin Kofin Champions League na kakar 2021/2022 ya zo da abin al’ajabi da kuma abin kunya.
Ƙungiyoyi biyu na Spain waɗanda a duniya babu kulob ɗin da ya kai su martaba a idon ƙwallon ƙafa, wato Real Madrid da Barcelona, sun haɗu da tsautsayin da ya keta masu rigar mutunci a wasannin da su ka buga a ranakun Talata da Laraba da dare.
Masana ƙabali da ba’adin ƙwallon ƙafa na ganin ba a taɓa yi wa babban kulob wulaƙanci kamar yadda ƙungiyar Sheriff ta Tirispol ta yi wa Real Madrid ba.
Baya ga cewa Sheriff ba ta taɓa fita gasar cin wani kofin Turai ba sai a wannan shekarar, kusan biliyoyin jama’a a duniya ba su ma taɓa jin sunan kulob ɗin ba kafin su ci Madrid a Spain.
Sannan kuma wata ‘yar ƙasa su ke da ta ɓalle daga Maldova, wadda ita Maldova ɗin ma ba ta amince da kafuwar ƙasar ba har yanzu.
Ci 2:1 da ‘Sharifan’ Tirispol su ka yi wa Madrid ba ƙaramin wulaƙanci ba ne. Ƙananan ƙungiyoyi sun taɓa wulaƙanta manyan ƙungiyoyi, kamar yadda Celtic ta a cikin shekarar 2012, ta yi wa Barcelona 2:1, a wasan da Barca ta taɓa ƙwallo sau 955, ita kuwa Celtic sau 166 kacal.
Cikin 2009 ma Rubin Kazan ta Rasha ta rafka wa Barcelona gora sau 2.
Sannan a cikin 2012, ƙungiyar BATE Borisov ta Belarussia ta wanke Bayern Munich da mari sau 3:1.
Amma dukkan waɗannan, wanda ya fi al’ajabi shirin tsarki da ruwan batir ɗin da Sheriff su ka yi wa Real Madrid. Saboda wannan ne karon farko na fitowar su har duniya ta san su.
Barcelona kuwa a cikin shekaru 4 zuwa yau, ta saba shan dukan tsiya a wajen manyan kulob. A wasanni 7 da ta buga a baya da Roma, Liverpool, Bayern Munich da PSG, an zabga wa Barca ƙwallaye kusan 30.
Abu mafi ciwo shi ne wulakancin da Benfica ta yi wa Barca a daren Laraba, a filin wasan Lisbon na Portugal, inda aka wanka mata ƙwallaye 3:0.
A filin wasan ne Bayern Munich ta zurara mata ƙwallo 8:2 a kakar 2019/2020.
A bisa dukkan alamu, ‘yar manuniya ta fara nuna cewa ƙungiyoyin ƙwallon Spain sun daina bai wa duniya tsoro.
Discussion about this post