Babbar kotun shari’ar musulunci ta Jihar Kano ta ki bayar da belin Sheikh Abduljababr Nasir Kabara.
A zama da kotun ta yi ranar Alhamis, alkalin kotun Mai shari’a Ibrahim Sarki-Yola, ya ki amincewa da bukatar da lauyan sheikh Kabara Barista Umar Muhammad ya gabatar.
A baya dama kuma lauyoyin Abduljabbar sun bukaci da a ba su takardar shari’ar, tare da kira ga masu kara da su gabatar da shaidunsu a zama na gaba domin a fara sauraron shari’ar.
Alkalin ya dage saurar karar zuwa ranar 14 ga watan October na gobe.
Idan ba a manta gwamnatin Kano ta maka shehin malami Abduljabbar Nasiru Kabara a babban kotun shari’a dake Ƙofar Kudu, jihar Kano.
” An kama Abduljabbar ne bayan samun rahoton aikata sabo, ganganci da katoɓara da ya yayi wanda ofishin Antoni Janar ya aika wa jami’an tsaro sannan da tafka saɓo kan Manzon Allah, Annabi Muhammadu SAW.
Idan ba a manta ba tun bayan muƙabalar da aka yi tsakanin shehin malamin da gamayyar malamai a Kano, wanda Abduljabbar bai iya amsa tambaya koda ɗaya ce da aka yi masa ba, ya fito ya rika cewa ba a yi masa adalci ba.
Wannan muƙabala an yi shine kai tsaya kowa yana ji sannan ana gani.
Bayan haka ya tabbata cewa Abduljabbar dai ruwa ne ya ƙare wa ɗan kada, amma ba shi da gaskiya sannan ya aikata kantamemen saɓo.
Ya nemi a yafe masa bayan an kammala muƙabalar, sai da kuma bayan ya koma gida sai ya koma ruwa tsindim ya sake fara sakin wasu bidiyoyi na sa ya na sukar malamai da muƙabalar da aka yi.