Shugaban kungiyar NARD dake aiki a asibitin koyarwa na Jami’ar Uyo Margaret Erhunmwunse ta bayyana cewa cututtukan dake kama zuciya na daya daga cikin manyan cututtukan dake kashe mutane a duniya da bincike ya nuna cewa a duk shekara mutum sama da miliyan 18 na rasa rayukansu a dalilin cututtuka irin haka.
Dakta Erhunmwunse ta fadi haka ne da take ganawa da manema labarai a taron ranar cututtukan dake kama zuciya mai taken “Amfani da fasaha wajen samun kula da hanyoyin gujewa kamuwa da cutar a duniya’.
Ta ce bullowar annobar korona ya sa masu fama da cututtuka irin haka na kamuwa da cutar cikin gaggawa.
“Zuwa asibiti domin yin gwaji da ganin likita, motsa jiki, cin abincin dake inganta garkuwar jiki, gujewa fadawa cikin damuwa, samun hutu, gujewa shan giya da busa taba sigari na cikin hanyoyin gujewa kamuwa da cututtukan dake kama zuciya.
“A rika zuwa ganin likita akai-akai musamman idan mutum na fama da hawan jini, ciwon siga da kiban jiki.
Sakamakon wani bincike da da hukumar NCS ta gudanar ya nuna cewa kashi 30 bisa 100 na mutanen Najeriya na fama da cututtukan dake kama zuciya musamman hawan jini.
NCS ta yi kira ga mutane da su kiyaye hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.
Wadannan hanyoyi kuwa sun hada da:
1. Mutum ya yawaita motsa jiki domin rage kiba a jiki
2. A rage yawan cin Kitse, sannan a yawaita cin kayan lambu da ganyayyaki.
3. A rage shan kayan zaki
4. A rage yawan cin gishiri.
5. Shan taba sigari da shan giya na kawo cutar hawan jini.
6. A yawaita zuwa asibiti domin yin gwaji akan cutar.
Discussion about this post