MATSALAR TSARO: Buhari na ganawa da jiga-jigan harkokin tsaron Najeriya

0

Shugaba Muhammadu Buhari na can ya na ganawa da Shugabannin Fannonin Tsaro a fadar sa.

Kamfanin Dillancin Labarai ya bayyana cewa ganawar ba za ta rasa nasaba da halin da ake ciki na barazanar rashin tsaro ba.

Sai kuma akwai yiwuwar tattauna batun ƙalubalen sarandar da ‘yan Boko Haram ke yi, wadda a yanzu haka ta zama wani alaƙaƙai.

Idan ba a manta ba, an ruwaito Gwamna Babagana Zulum da Shuhun Barno su na nuna damuwar cewa jama’ar da Boko Haram su ka karkashe wa iyalan su da dangogin su, zai yi wuya su sake karɓar su idan sojoji na sakin su bayan sun yi saranda ɗin.

Kwanan nan dai sojojin Najeriya sun matsa ƙaimi wajen kai wa Boko Haram hare-haren da tilas ɗaruruwan su ke ci gaba da miƙa wuya.

Waɗanda su ka halarci taron da Shugaba Buhari sun haɗa da Mataimakin sa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa da Mashawarci kan Harkokin Tsaro.

Akwai Ministan Tsaro, Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Ministan Harkokin Waje da na Cikin Gida.

Sai kuma Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, na Ƙasa da na Ruwa da na Sama.

Akwai kuma Sufero Janar na ‘Yan Sandan Najeriya shi ma a cikin mahalarta taron.

Share.

game da Author