KUDU TA DAGULE: An yi wa sufeton ‘yan sanda da wasu mutum shida kisan gilla a Imo

0

An yi wa mutum bakwai kisan gilla a Jihar Imo, lokacin da ‘yan bindiga su ka yi wa jerin gwanon ma’aikatan Kamfanin Haƙo Mai na Shell kwanton ɓauna.

Shida daga cikin waɗanda aka kashe ɗin dai ma’aikatan Lee Engineering Company ne, wanda ke aiki a ƙarƙashin Shell. Sai na cikon bakwai ɗin kuma wani Sufeton ‘Yan Sanda ne.

Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sanda a Jihar Imo, Mike Abattam ya shaida wa PREMIUM TIMES faruwar lamarin a ranar Laraba.

Kamar yadda ya ce an kashe matafiyan a ranar Litinin, ciki har da sufeton ‘yan sanda mai ba su kariya.

“Kwanton ɓauna aka yi masu. Maharan sun fito daga cikin daji su ka buɗe masu wuta. Kuma daga duk a cikin mota ɗaya su ke. Har da sufeton ‘yan sanda mai ba su kariyar, shi ma an kashe shi.”

“Har zuwa yanzu dai ba za mu iya cewa ga waɗanda su ka yi wannan mummunan kisa ba. Binciken da ake yi ne kaɗai zai iya tabbatar da waɗanda su ka yi kisan.” Inji Abattam.

Shi ma Kakakin Kamfanin Shell, Bamidele Odugbesan, ya ce ma’aikatan su na kan hanyar su ce ta zuwa Assa North domin aikin gas.

Odugbesan ya ƙara da cewa Shell ya rufe wurin aikin, “matakin kariyar sake faruwar haka.”

“Muna cikin ɓacin rai matuƙa da tashin hankalin wannan mummunan kisa da aka yi.”

Tun bayan a tsagerun IPOB su ka fara tayar da ƙayar baya su ke ta kashe-kashen jami’an tsaro da lalata dukiyoyin gwamnati a yankin Kudu maso Gabas.

Share.

game da Author