Najeriya ta fara samu karuwa a yaduwar cutar korona bayan sakamakon bincike ya nuna bullowar zazzafar nau’in cutar ‘Delta’ a kasan.
Bisa ga alkaluman da hukumar NCDC ta fitar daga ranar Litini zuwa Talata mutum 352 ne suka kamu sannan mutum daya ya mutu a kasar nan.
A ranan Litini mutum 146 ne suka kamu sannan mutum daya ya mutu.
Alkaluman sun nuna cewa mutum 134 sun kamu a jihar Legas, Ondo -3, Kwara-2, Cross Rivers-2, Abuja-2, Oyo-1 da Rivers-1.
A ranar Talata mutum 206 ne suka kamu sannan babu wanda ya mutu a cikin sa’o’i 24 a ƙasan.
Alkaluman sun nuna cewa jihar Legas ta ƙara zama jihar da ta fi kowace jihar samun yawan mutanen da suka kamu da cutar da mutum 132, Akwa-Ibom -56, Ekiti-5, Delta-3, Rivers-2, Enugu-2, Jigawa-2, Katsina-2, Gombe-2 da Abuja-2.
Mutum 169,884 ne jimlar yawan mutanen da suka kamu da cutar sannan mutum 2,128 ne suka mutu jimla a kasar nan.
An sallami mutum 164,733 sannan akwai mutum 3,000 dake killace a dalilin kamuwa da cutar.
Hukumar NCDC ta ce an yi wa mutum miliyan 2.4 gwajin cutar daga cikin mutum miliyan 200 dake zama a kasar nan.
Bayan haka gwamnati ta gargaddi mutane da su mai da hankali wajen kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da korona musamman yanzu da aka samu labarin bullowar sabuwan nau’in cutar ‘Delta’.
Gwamnati ta yi wa mutane barka da sallah sannan ta yi kira da a kare juna yayin da ake shagulgulan sallah daga kamuwa da cutar.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin cewa Najeriya za ta karbi kwalaben ruwan maganin rigakafin cutar korona 41,282,770 a karshen watan Satumba 2021.
Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya ce maganin rigakafin na Oxford-AstraZeneca, Pfizer-Bio-N Tech/Moderna da Johnson & Johnson (J&J) na daga cikin miliyan 41 din da Najeriya za ta karba.
Zuwa yan su hukumar NPHCDA ta ce mutum miliyan 3.9 sun yi allurar rigakafin korona zango na farko a kasar nan.
Discussion about this post