Gwamnatin jihar Kano ta bada kwangilan gina rijiyar burtsatse da za ta kashe naira miliyan 18.1 a makarantun gwamnati uku da makarantun tsangaya guda 10 a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimin jihar Malam Aliyu Yusuf ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai a garin Kano ranar jajibirin Sallah.
Yusuf ya ce za a gina rijiyar burtsatsen ne a tsangaya da ake karantar da Almajirai dake Bichi, Kiyawa, Garo, Albasu, Gaya, Warawa, Tsakuwa, Kibiya, Kanwa da Dandishe.
Sannan da makarantun sakandaren gwamnati dake Tudun Maliki, Kwalejin GTC Ungoggo da kwalejin ‘First Lady’, Mariri.
A karshe Yusuf ya ce za ayi haka ne domin sawwake wa ɗalibai a lokacin da suke karatu.