Jami’an Kwastam a Najeriya sun gano harsasan bindiga 200,000 a shekarar 2018 ne ba a 2021 ba – Binciken Dubawa

0

Wani rahoton da ake yadawa a shafukan sada zumunta da wasu shafukan labarai na zargin cewa jami’an kwastam a Najeriya sun kama wata mota dankare da harsasai 200 000 a jihar Neja, a kan iyakar Wawa-Babana, yayin da take hanyar zuwa birnin Onitsha daga Jamhuriyar Benin ranar 10 ga watan Yulin 2021

Wani rahoton da ke daukar hankali a shafukan sada zumunta da na labarai na zargin cewa kwanan, jami’an kwastam a Najeriya suka kama wata mota dauke da harsasai 200,000. Rahoton ya ce motar mai lambar Legas AKD904X ta shigo hannun jami’an ne a garin Wawa-Babana da ke jihar Neja, kan iyakar jihar da Jamhuriyar Benin.

Banda shafukan sada zumunta da wadansu taskokin da suka wallafa rahoton. CKNNigeria ta wallafa labarin tana cewa “Jami’an Kwastam sun kama motar da ke dauke da harsasai 200,000 a jihar Neja.” Labarin bai tsaya nan ba, ranar 11 ga watan Yulin 2021 jaridar Naijanews ita ma ta sake wallafa labarin da kanu makamancin na CKNNigeria tana bayyana shi a matsayin wani abun da ya faru kwanan nan.

A shafin Facebook, jaridar Vanguard ma ta sake raba labarin a shafinta ranar 11 ga watan Yulin 2021 har ma wani ya yi tsokaci a karkashin labarin yana cewa “Himma dai jami’an tsaro” wani kuma ya yi tambaya mai cewa “Shin wai me kasar nan ke kokarin zama ne?”

Yayin da jama’a ke cigaba da yada wannan labarin a shafukan yanar gizon, wadansu na zargin a shekarar 2018 lamarin ya afku ba 2021 ba. Wannan rashin tabbas ne ya sanya Dubawa gudanar da binciken tantance shekarar da aka gano wadannan harsasai.

Tantancewa

Da farko, Dubawa ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na yankin jihohin Neja da Kogi a ofishin Kwastam na Najeriya, Mr Emmanuel Tangwa wanda tabbatar mana cewa wannan abu ya faru shekaru uku da suka gabata kuma yadda ake yada labarin yanzu yana yaudarar jama’a ne kawai.

“Tabbas mun yi wannan aiki kuma a wancan lokacin kafofin yada labarai da yawa sun dauki labarin sai dai sabanin da ake samu shi ne lamarin ya afku ne a shekarar 2018 ba kwanan nan ba yadda ake rawaitawa, ya ce”

Mr Tangwa ya kuma kara da cewa hukumarsa ta fitar da sanarwar manema labarai domin fayyace hakan. DUBAWA ta sami kofi na wannan sanarwa a whatsapp wanda ya bayyana cewa an kama motar harsasan a shekarar 2018 ne ba 2021 ba.

Dubawa ta sake gudanar da bincike a shafin google dan tantance sadda labarin ya fara fita. A nan ma ta sami tabbacin cewa labarin ya fara fita a 2018 kuma kafofin yada labarai da yawa sun dauki labarin.

Gidan talbijin din Channels ma ya sanya labarin a shafin shi na yanar gizo. Jaridar TheCable ma ta wallafa labarin a watan Yulin 2018 tana cewa “Kwastam: Mun kama wata mota dauke da harsasai 200, 000

A karshe

Duk da cewa gaskiya ne jami’an kwastam a yankin jihohin Neja da Kogi sun kama mota cike da harsasai 200, 000 abun ya faru ne a shekarar 2018 ba 2021 kamar yadda ake yadawa ba.

Share.

game da Author