Shin akwai illa saka wayar hannu a karkashin matashin kai a kwana a kai? – Bincken DUBAWA

0

Zargi: Wasu na zargin cewa kwanciya da waya a karkashin matashin kai na da hadari ga lafiyar mutum

Yawancin mutane musamman matasa wadanda suka fi amfani da wayoyinsu sukan yi baci da wayar kusa da su musamman a karkashin matashi. Suna yin haka ne dan daukar wayar cikin sauki ko da ta buga.

To sai dai kwanan nan jaridar Pulseng ta wallafa wani labari kan dalilin da ya sa ajiye wayar a karkashin matashi ke tattare da hadari. Labarin da ta kira “Dalilin da ya sa baci da waya a kan gado ke da hadari ga lafiya.”

Wannan ya janyo martanoni masu goyon bayan zargin. Domin a cewar labarin, kwana da waya kusa da kai na da lahani ga wasu fannonin jikin mutun, yana hana jiki sarrafa wadansu sinadarai masu mahimmanci, ga jiki, kuma yana iya lalata kwakwalwa.

Labarin ya bukace mutane su rika ajiye wayarsu a waje mai nisa da su, wato akalla kafa daya daga inda suke kwanciya idan har ba za su kashe wayar ba.

Wadansu masu amfani da shafin twitter irin su SC (@sgxphotos) da Redheaddevilchild (@redheaddevilch1) sun yi tsokaci dangane da batun sun cewa “Wannan na nufin zan sami cutar cancer ko maruru a kwakwalwa na dan ina kwana da waya a karkashin matashi?”

Shin, kwana da waya a karkashin matashi na da hadari?

Tantancewa

Wannan mai binciken (wanda ya rubuta wannan labarin) ya gano cewa an dade ana wannan tambayar musamman a wani shafin yanar gizo mai suna “Quora” inda Amurkawa ke yawan rubuta tambayoyi dan sauran masu amfani da shafin su basu amsa.

Wani daga cikin masu amfani da shafin mai suna Owen Saltvold ya amsa tambayar da cewa kwana da waya a karkashin matashi ba shi da wani hadari ga kwakwalwa, ko ga lafiyar jikin dana dam.

Haka nan kuma akwai wani bidiyo a shafin Facebook wanda shi ma ya bayyana hadarin kwanciya da wayar a karkashin matashi kuma ya zuwa lokacin da muka rubuta wannan labarin, mutane sun kalli bidiyon har sau 226,000

A cewar wani shafin da ke illimantar da jama’a kan fasahohi da yanar gizo mai suna Technopedia, wayar hannu, na’ura ce mara igiya wadda ke taimakawa masu amfani da ita su kira mutane, su ma a kira su. Sai dai yayin da wayoyin da aka fara sarrafawa a duniya ne suka rika kira da amsa waya, yau an wayi gari wayoyin da ake sarrafawa na yin abubuwan da suka fi haka, domin ana iya binciken abubuwa a yanar gizo, ana iya yin wasanni, akwai kamara ta daukar hotuna, ana iya kallon hotunan bidiyo, ana iya nadan muryoyi da kuma sauran rubuce-rubuce.

Wayar hannu na aiki da hanyar sadarwar salula, wadda ke hada tashoshi daban-daban a birane da kauyuka. To sai dai hanyoyin sadarwar da ake amfani da su a wayoyin hannun da ake kira “smart phones” sun sauya sosai yanzu.

A ko da yaushe jikinmu na ma’amala da wasu kwayoyin lantarkin da ba’a gani (Electromagnetic radiation EMR) wadanda ake samu yayin da ake amfani da naurorin da ke amfani da wutar lantarki, kamar hanyoyin wuta, lantarkin da ake sanyawa a gidaje da ma sauran fasahohin da ake amfani da su a rayuwar zamani. Alal misali akwai na’urar wanke kwanoni, akwai na dimama abinci da ma agogon da akan ajiye a gefen gado da wayar hannu wanda mukan kanga a jikin kunne – wata sa’a na tsawon sa’o’i masu yawan gaske a rana – kullun ma’amalar jikinmu da ire-iren wadannan kwayoyi karuwa yake yi kuma ana zargin hakan na kasancewa barazana ga lafiyarmu.

Ga wadansu wannan hadarin ya danganci kwayoyin lantarkin da ke fita daga wayoyin hannu – Wato daga wayoyin hannun da muke dauke da su har zuwa wadanda ke kan babbar tashar wayoyin sadarwar, domin akwai binciken da ke danganta su da samun kumburi a kwakwalwa, da lalata kwayoyin halitta da ma sauran cututtukan da ke kama da wadannan.

Wayoyin hannu suna aiki da mitoci irin na rediyo ne, wadanda ke da karamin karfi. Iyakacin karfin su na tsakanin mitoci 450 da 2700 MHz idan har sun yi karfi sukan kai 0.1 zuwa 2 bisa ma’aunin watts. Wayar tana iya aikawa da sigina idan har an kunna ta. Karfin wannan siginan da take da shi yakan ragu idan mutun ya yi nisa da ita.

Wanda ke mafani da wayar da ke da tazarar 30-40 cm daga jikinshi – misali idan yana aikawa da sakon text, ko yana bincike a yanar gizo ko kuma yana amfani da abin saurare na kunne ba zai yi ma’amala da kwayoyin lantarkin kamar yadda wanda ya sa wayar a kai ko a kunne zai yi ba.

Wani masani a fanin naurorin da ke daukar hoton cikin jikin mutun a jami’ar kimiyyar ayyukan asibitin da ke jihar Ondo (UNIMED), Dr Femi Akindeju ya ce ba a tantance a hukumance cewa kwana da waya a karkashin matashi na da hadari ga lafiya ba, ya ce bacin haka, kwayoyin lantarkin da wayoyi ke fitarwa ba su da yawan da za su iya yin lahani ga lafiyar mutun.

Ya ce “Idan ana batun kimiyya ta makamashi da lantarki, wayoyi na amfani da kwayoyin lantarkin da aka fi sani da radio waves ne. Akwai kwayoyin lantarki iri-iri, kuma akwai mizanin da muke amfani da shi wajen auna karfin kwayoyin lantarkin. Da haka ne muke sanin masu karfi da marasa karfi. Radio waves din da ake samu a kan wayoyin basu da karfi, muamman idan aka hada su da masu karfi kamar na yin X-ray ko kuma naurar daukar hoton cikin jikin dan adam.”

“matsalar kwayoyin lantarki ita ce suna iya janyo abin da ake kira ionization wanda wani yanayi ne inda kwayoyin lantarki ke iya baiwa kwayoyin jikin mutun (wadanda ba ruwansu da lantarki) irin karfin da ake samu a kwayoyin lantarki musamman idan suna da karfi. Sai dai radio waves wadanda ake samu a wayoyin hannu ba su da irin karfin da za su shafi kwayoyin jikin mutun.

“Zan dai ba da shawarar cewa mutane su guji dadewa a kan wayoyinsu amma dan sa wa a karkashin matashi ba zan ce yana tattare da wani hadari ba domin tsawon lokacin da ake bukata mutun ya yi ma’amala da wadannan kwayoyin lantarki kafin su yi lahani a jikinshi na da yawa. Dan haka zai yi wuya wayar hannun ta kasance da lahani,” ya ce.

Wani mai daukar hoto (ko kuma radiographer a turance) a asibitin UCH kuwa Dr Taiwo Orimogunje ya yadda cewa kwanciya da wayar a karkashin matashi na da hadari. Dr Orimogunje ya ce “ kowa ya san cewa na’urori irin wayoyin hannu na fitar da wasu kwayoyi na lantarki kuma wadannan na iya yin lahani ga kwakwala musamman na yara. An kuma ce suna janyo kumburi a kwakwalwa dan haka yana da hadari dan zai iya janyo kumburin da zai haifar da kansar da ake kira Meningioma wanda ke shafar kwakwalwa.”

Sai dai kuma likitan kwakwala Dr Taofik Sunmonu wanda ke aiki da Federal Medical Center Owo a jihar Ondo ya ce babu wata hujjar da ta ba da tabbacin hakan, amma abu ne wanda mutane suka yadda da shi, na wani tsawon lokaci yanzu.

“mun dade muna jin wannan zargin tun kafin yanzu, saboda akwai kwayoyin lantarkin da ke fita daga wayar hannu da ma sauran na’urori, amma yawan ya banbanta. An kuma yadda cewa idan waya ta dade a kusa da mutun sosai yawan kwayoyin lantarkin zai kasance daban kuma zai iya lahani. A yanzu haka dai abubuwan da muka sani a zahiri ke nan.”

“Bayan haka, ba dabi’a mai kyau ba ne a sa wayoyi a kai saboda duk wani abin da ke dauke da kwayoyin lantarki zai iya yin lahani ga jikin mutun dan haka dace mu rika kwana da shi ba, gara kawai mu kai shi nesa idan har zamu kwanta,” ya ce.

A karshe

Duk da cewa babu kwakkwarar hujjar da ta tabbatar cewa sanya waya a karkashin matashi na da yin lahani ga lafiyar mutum, akwai tabbacin cewa ita kanta waya na fidda sinadarin wutar lantarki daga jikin ta, don haka ana bayar da shawarar takaita amfani da wayar da kuma a rika ajiye su a wani wuri na daban kafin a kwanta mai makon a karkashin matashin kai.

Share.

game da Author