Karin wasu daliban makarantan Bethel 4 sun arce daga hannun ‘yan bindiga, saura dalibai 83

0

Wasu daliban makarantar ‘Bethel Baptist’ dake Maraban Damishi a karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna su hudu sun arcewa daga hannun ‘yan bindigan dake tsare da su a daji ranar 25 ga Yuli.

Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya CAN reshen jihar Kaduna John Hayab ya sanar da haka ranar Litini da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a garin Kaduna.

“Mun samu karin wasu dalibai guda huku da suka kubuto daga hannun ‘yan bindigan dake tsare da su a daji kuma har an damka su hannun iyayen su.

Hayab ya tabbatar cewa har yanzu akwai sauran daliban makarantar 83 dake tsare a hannun ‘yan bindigan.

Idan ba a manta ba a ranar Lahadin da ya gabata ne ‘yan binda suka sako daliban makarantar Bethel Baptist’ guda 28 a Kaduna
An rika kiran sunayen su ɗaya bayan ɗaya ana mika su ga iyayen su.

A wani bidiyo da muka gani yaran duk sun galabaita, babu sauran ƙarfi a jikin su, iyayen kuma suna ta koke-koke suna rungumar ƴaƴan su.
Sai dai babu tabbacin ko an biya kudin fansan wadannan dalibai kafin aka sakodu.

A kwanakin baya PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda wasu daliban makarantar biyu da suka arce daga hannun ƴan bindigan bayan an aikesu su yo ice.

Sannan kafin nan gidan jaridar ta rawaito cewa wani dalibin makarantar tare da wasu mutane biyu sun gudo daga hannun ‘yan bindigan.

Sace yaran makarantar Bethel Baptist shine karo na hudu da ‘yan bindiga ke sace ‘ya’yan mutane a makarantu a jihar Kaduna

Share.

game da Author