Gwamna Matawalle ya bai wa Majalisar Dokoki da Kotunan Zamfara ‘yancin gashin kan su

0

Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya bai wa Majalisar Dokokin jihar da Kotunan Jihar Zamfara ‘yancin cin gashin kan su.

A ranar Alhamis ce Matawalle ya sa hannu kan dokar da ta cire Majalisa da kotuna da ɓangaren Shari’a na jihar daga ƙarƙashin ikon gwamna.

Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna Matawalle, Yusuf Idris ne ya sanar da haka cikin wata sanarwar da ya tura wa manema labarai a ranar Alhamis.

Ya ce gwamnan ya sa hannu ne a lokacin wani ƙwarya-ƙwaryar bikin da aka yi a Gidan Gwamnatin Jihar.

“Ban ga dalilin da za a tsaya ana ta ruwa rana wajen hana Majalisa da ɓangaren Shari’a na jiha zaman kan su ba.

Sa hannun dai na nufin cewa dukkan kuɗaɗen su za su riƙa je masu ne kai tsaye daga aljihun gwamnatin tarayya, ba tare da sun bi ta hannun gwamnatin jiha ba.

Idan ba a manta ba, kotunan ƙasar nan sun shafe sama da watanni biyu a kulle a baya, saboda dambarwar ƙin sa wa dokar hannu da gwamnoni su ka yi, bayan Shugaba Buhari ya sa hannun amincewar ba su ikon su kai tsaye.

Cikin watan jiya ne PREMIUM TIMES Hausa ta ruwaito Tambuwal na cewa Buhari ya wuce-makaɗi-da-rawa, dangane da azarɓaɓin sa wa Dokar Musamman ta Shugaban Ƙasa ta 10 hannu, wacce ta bai wa Majalisar Dokokin Jihohi da Kotunan Jihohi ikon cin gashin kai.

Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto, ya bayyana cewa Buhari ya wuce-makaɗi-da-rawa wajen busar-iskar da ya yi ya saka hannu kan Dokar Shugaban Ƙasa ta 10.

Wannan doka dai ita ce ta tabbatar wa kotunan jihohi da Majalisun Dokokin Jihohi ‘yancin cin gashin kan su.

Wanann ‘yanci ya na nufin Gwamnatin Tarayya za ta daina tura kuɗaɗen da ta ke bai wa Majalisun Dokoki da Kotunan Jihohi ta hannun gwamnonin jihohi.

Wato za su riƙa karbar kuɗaɗen su kai-tsaye daga gwamnatin tarayya.

Share.

game da Author