Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa mahara sun kashe mutum 18 a wani hari da aka kai a kauyen Tsauwa dake karamar hukumar Batsari.
Kakakin rundunar Gambo Isah ya sanar da haka ranar Laraba yana mai cewa maharan sun afka kauyen a cikin daren Litinin.
Mazauna kauyen sun ce akwai yiwuwar maharan sun kawo harin daukan fansa ne domin a ranar Juma’ar data gabata jami’an tsaro sun fatattaki wasu mahara da suka kawo farmaki kauyen.
A wannan rana jami’an tsaron sun kashe mahara uku daga cikin su.
Mazaunan kauyen sun ce maharan sun cinna wa gidaje da rumbunan hatsi wuta sannan sun saci dabbobi da dama daga kauyen kafin suka koma daji.
Isah ya ce a yanzu haka jami’an tsaro na farautar maharan a can cikin daji.
Discussion about this post