Wasu ‘yan majalisar Amurka masu faɗa-a-ji, sun shirya hana Amurka ci gaba da sayar wa Najeriya jiragen yaƙi, saboda damuwar da su ke nunawa cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ɗauki hanyar rikiɗewa ta koma gwamnatin kama-karya.
Hakan ya zo ne daidai lokacin da ƙasar nan ke fama da matsalolin tsaron da ke neman gagarar daƙilewa, kama daga yaƙin Boko Haram da ya shafe tsawon shekaru 12 ana gumurzu da Boko Haram, hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane.
Masu sharhi na ganin hare-haren ‘yan bindiga shi ma zama yaƙin sunƙuru kamar Boko Haram.
Bugu da ƙari kuma yayin da ake fama da ‘yan awaren Biafra’, a Kudu Maso yamma can ma masu rajin neman ɓallewa sun bayyana.
Manyan ‘yan majalisar musamman ‘yan Kwamitin Harkokin Ƙasashen Waje na Democrat da Republican, duk su na matsa wa Gwamnatin Joe Biden ta canja tunani kan yarjejeniyar sayar wa Najeriya jiragen yaƙi da makamai domin daƙile tashe-tashen hankula a Najeriya.
Cikin Yuni Shugaban Kwamiti Bob Menendez ya shaida wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Anthony Blinken cewa “a canja tunanin sayarwa Najeriya kayan yaƙin baki ɗaya.”
Jaridar Foreign Policy ta ce takardun bayanan da ta ci karo da su sun nuna an nemi a tsaida shirin sayar wa Najeriya kayan yaƙin da aka yi yarjejeniyar sayar mata a lokacin gwamnatin Donald Trump.
‘Yan majalisar na Amurka sun nuna damuwa kan irin kisan da aka yi wa ɗaruruwan ‘yan Shi’a a Kaduna cikin 2015.
Sai kuma kisan da aka yi wa masu zanga-zangar #EndSARS cikin 2020.
Idan ba a manta ba Gwamnantin Barack Obama ta soke sayar wa Najeriya makamai bisa dalilin kisan da aka yi wa fararen hula cikin 2014.
Tsohon Jakadan Najeriya a Chana, Aminu Wali ya ce soke yarjejeniya damfara ce da cin amana.