Neman aure ya yi sanadiyyar mutuwar Nabajallah, kasurgumin dan bindiga a Katsina

0

Wani kasurgumin dan bindiga da ya addabi yankin Dungun Mu’azu dake karamar hukumar Sabuwa, jihar Katsina mai suna Nabajallah ya gamu da ajalinsa bayan wasu abokan hamayyar sa sun diran masa babu shiri sun kashe a gidan sa dake Sabuwa.

Wani da yasan yadda abin ya faru ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa gasar neman auren wata yarinya ce ya hada bangaren Nabajallah da bangaren da basu ga maciji rikicin da ya kaiga an hallaka shi.

” Wani daga cikin dakarun Nabajallah ne yake neman wata budurwa da aure a daidai wani saurayi dan bangaren adawa shima ya na neman wannan yarinya da aure.

” NabajaAllah yayi ruwa yayi tsaki sai da dole da karfin tsiya yaron sa ya yi nasara wajen samun wannan yarinya. Dalilin haka ne yan bangaren adawa suka fusata suka ce lallai sai sun maida martani, wato sai sun ga bayan sa.

” Daga nan ne suka dira gidan sa da sassafe a lokacin ba aya tare da mafi yawa daga cikin yaran sa suka hallaka shi. Sai dai kuma daga baya yaran Nabajallah din sun bi bayan su sun kashe mutum uku cikin su.

Jihar Katsina, Kaduna da Zamfara sune jihohin da ayyukan yan bindiga ya fi tsanani a yankin Arewa Maso Yamma.

A kusan Kullum sai an yi kisa ko kuma an yi garkuwa da mutane masu yawa.

Share.

game da Author