Ba wanda ya isa ya sa mu soke ko mu sassauta dokar hana gararambar kiwon shanu – Gwamna Ortom

0

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya ce hare-hare ba ƙaƙƙautawa da makiyaya ke kaiwa a jihar da yawan yi masa sharri, ba za su sa gwamnatin sa ta soke ko ta sassauta dokar hana kiwon shanu a faɗin jihar ba.

Ya ce Jihar Benuwai ta riga ta kafa doka, ko dai a daina kiwo kowa ya ciyar da dabbobin sa a garke kuma ya killace su, ko kuma doka ta hau kan sa.

Ortom ya yi wannan ƙarin bayani a Makurɗi, lokacin da ya ke duba aikin yi wa Gidan Gwamnati kwaskwarima.

Ya ce ana ta matsa masa lamba wai lallai ya soke dokar hana kiwo sakaka da ya ƙaƙaba wa makiyaya.

“Ba mu janye ko sokewa ko sassauta dokar hana kiwo sakaka a jihar Benuwai ba. Kuma ba gudu ba ja da baya.”

“Tun daga ranar da na sa wa dokar hana gararambar kiwo a jihar Benuwai hannu cikin 2017, har zuwa yau babu inda na ce na kori Fulani, Hausawa, Igbo ko Yarabawa a Jihar Benuwai.

“Cewa na yi kowa na da ‘yancin ya yi halastaccen hada-hadar kasuwanci da harkokin sa cikin Jihar Benuwai. Wannan doka alheri ce ga su kan su Fulani makiyaya, manoma da duk wani ɗan Jihar Benuwai da ke yin harkokin sa bisa yadda tsarin da doka ta amince ya yi.”

Ortom ya ce ko kashe shi aka yi wannan doka ta rigaya ta zauna daram, ba za a soke ta ko kankare ta ba.

“Dokar nan ba don amfanin ni Samuel Ortom aka kafa ta ba. An kafa ta don amfanin al’umma. Shi ya sa na ke bai wa Shugaba Buhari shawara daina tsagalgalewa kan lallai sai an ci gaba da kiwo sakaka ana gararamba da shanu a faɗin ƙasar nan.

“Saboda makiyaya na kiwo sakaka a ƙasar nan, ba ya ci gaba da haifar da komai sai rikice-rikice, hargitsi da ɗaukar doka a hannun waɗanda doka ta hana su ɗauka.”

“Gararamba ana yawo da shanu da sunan kiwo tsohuwar ɗabi’a ce. Shi ya sa mu ma don mu wanzar da zaman lafiya, mu ka ce kai ko Bahaushe ne, ko Bafulatani ko Tivi ko Ƙabilar Igbo, kai kowace ƙabila ka ke, to wannan dokar hana gararamba da shanu ana kiwo ya hau kan ka.” Inji Ortom.

Share.

game da Author