KANO: Hizbah ta haramta wa teloli da masu kantina amfani da mutum-mitimi wajen tallata kayan su

0

Hukumar Hizbah ta Jihar Kano ta haramta wa teloli da masu shaguna amfani da mutum-mitumi wajen tallafa samfuran ɗinkunan su, ko kayan sayarwar su.

Shugaban hukumar Sheikh Haruna Ibn Sina ne ya bayyana haka, inda ya ce kafa mutum-mitimin mai kama da gunki, ya saɓa wa Musulunci.

A Kano dai yawancin teloli da masu kantinan sayar da kayan zamani su na amfani da mutum-mutumin roba, wanda ake sa wa kaya, domin kwastomomi su ka yadda samfurin suturar ke bin dirin-jiki.

Sai dai kuma daga ranar Laraba Hisbah ta yi hani ga yin amfani da su, kuma hukumar ta ce za ta fara bi shagunan teloli da kantinan sayar da kayayyakin zamani ta na kama duk wanda ya karya wannan doka.

Hukumar Hizbah dai tun farkon kafa ta ne ta haramta sha, sayarwa da safarar giya a fadin jihar.

Haka kuma Hukumar KATOTA a Kano, ta maida lasisin tuƙa Keke NAPEP Naira 100,000 daga naira 8,000.

Hukumar Kula da Babura da Motoci ta Jihar Kano (KAROTA), ta yi wa lasisin tuƙa A Daidaita Sahu, wato Keke NAPEP ƙarin naira 92,000.

Shugaban Hukumar KAROTA, Baffa Babba Ɗan’Agundi, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa daga yanzu duk wanda zai yi rajistar lasisin ba shi damar tuƙa A Daidaita Sahu, sai ya biya naira 100,000 maimakon naira 8,000 kacal da ake biya kafin a yi ƙarin.

Ya sha alwashin cewa jami’an KAROTA za su fara bi kan titina su na damƙe duk wanda ba shi da lasisi da aka kama ya na tuƙa A Daidaita Sahu a Jihar Kano.

Ya ce hukumar tuni ta umarci direbobin A Daidaita Sahu su yanki lasisin tuƙi na naira 8,000, amma su ka yi kunnen-uwar-shegu da umarnin.

Tsauraran Dokokin A Daidaita Sahu A Kano:

1- Ba a yarda a ɗauki mace da namiji tare ba (amma tuni aka yi fatali da wannan dokar, ana karya ta).

2 – Tilas da dare sai ka kunna fitila a cikin babur ɗin.

3 – Komin tsananin ruwa ko sanyi ko iska, ba yarda a ɗaura labulen hana fasinjoji jiƙewa ba.

Share.

game da Author