Sarkin Daura Umar Faruk Umar, ya bayyana cewa ƴan Najeriya sun yi babbar sa’a da katarin samun Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaba.
Da ya ke jawabin karɓar babban baƙo lokacin da Shugaba Buhari ya kai masa ziyara, Sarkin Daura ya ce da ba Buhari ke mulkin ƙasar nan kawo yanzu ba, da an bani an lalace.
“Najeriya ta yi dacen hawan ka mulki. Ba wai ina faɗar haka ba ne don na faranta maka rai ba. Amma idan da ba ka hau mulki ba, to da ƙasar nan an bani an lalace.
“Da ba ka hau mulkin ƙasar nan ba, to ba na jin za mu kawo har zuwa yau.”
“Allah ya albarkace mu da samun nagartaccen mutum. Saboda haka mu na alfahari da cewa daga cikin mu ka fito.
“Kuma zuwan da ka ke yi ziyara gida na nuna irin mutumtakar ka da nagarta irin taka da kyawawan ɗaɓi’un ka. Mun gode da ka ke ware lokaci ka na zuwa, duk kuwa da irin ɗimbin muhimman ayyukan da ke gaban ka.”
Sarkin Daura ya kuma jinjina wa Shugaba Buhari kan ayyukan raya ƙasa da ya sa a gaba. Amma kuma ya yi kira a ƙara himma a ɓangaren tsaro.
A wurin ya bayyana sarautar Talban Daura ga Yusuf Buhari, ɗan Shugaba Buhari. Sai Musa Daura kuma Ɗanmadamin Daura.
Kuma ya tantance sarautar Talban Hausa daban da Talban Daura. Sarkin ya ce sarautar Talban Hausa ya bai wa Shugaban Gini, kuma ba ɗaya ta ke da ta Talban Daura ba.
Sarki ya ce zai sa ranar da rza a yi wa su Yursuf bikin naɗin sarauta, kafin ranar bikin auren sa.
A ƙarshe ya ceci Masarautar Daura ta amince za ta ƙirƙiro Gundumar Hakimi sukutum a mahaifar Shugaba Buhari, wadda za a yi wa hedikwata a Dimorkul.
Da ya ke jawabi, Buhari ya ce kada a riƙa yi masa ko jami’an gwamnatin sa ‘ɗan ihisani’ ko hasafin kyautar kuɗaɗe don neman wata alfarma ko ladar karɓar aikin kwangila.
Shugaba Muhammadu Buhari ya gargaɗi ‘yan kasuwa, ‘yan kwangila da sauran manyan Najeriya masu ƙumbar susa su guji ƙoƙarin yi masa kyauta ko shi ko jami’an gwamnatin sa.
Da ya ke jawabi a Fadar Sarkin Daura, lokacin da ya je gaisuwar fada, Buhari ya ce, “ba na buƙatar kuɗin ku. Ku ɗauki kuɗin ku yi wa je ku taimaki jama’a mabuƙata da su, maimakon su riƙa bai wa ma’aikatan sa na ofis ko jami’an gwamnatin sa kuɗaɗe.
Buhari ya kai gaisuwar fada tare da ɗan sa Yusuf Buhari, wanda aka naɗa Talban Daura’ sai kuma Musa Daura da aka naɗa Danmadamin Daura.
“Ba mu buƙatar kuɗaɗe daga wani mutum ko wata ƙungiya a matsayin ladar wani aiki ko kwangilar da aka ba shi. Su tuna akwai ayyukan inganta rayuwar al’ummar da za su iya yi da kuɗaɗen.” Inji Buhari.
Buhari ƙara da cewa ya na so ya riƙa kai ziyara Daura akai-akai, amma saboda tsadar kuɗaɗen da ake kashewa wajen zirga-zirgar tafiye-tafiyen Shugaban Ƙasa da kuma karakainar kai jami’an tsaro cikin yanayin da ba su saba ya, shi ya sa ya ke taƙaita yawan zuwan.
“Kowa ya san mu da noma, domin Ni ma ina da gona a nan Daura. Zan so na riƙa zuwa duk bayan mako biyu, kuma ba wanda zai hana ni zuwa. Amma gara a riƙa kashe kuɗaɗen jama’a ana gina wa yaran su makarantu da asibitoci da a riƙa kashe kuɗaɗen wajen karakainar zuwa na ganin gida.”
Sarkin Daura ya ce zuwa ganin gida da Buhari ke yi, ya nuna matuƙar kyawawan halaye da ɗabi’un sa.