Ainihin dalilin da ya sa EFCC ta kama Tanko Almakura da Matarsa

0

Hukumar EFCC ta Kama tsohon gwamnan jihar Nasarawa wanda sanata ne yanzu a da matarsa ranar Laraba.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa zuwa daren nan tsohon gwamnan da matarsa na gaban hukumar yana amsa tambayoyi.

Duk da ba a bayyana dalilin yi musu wannan kame ba, ana zaton cewa binciken wasu bacewar kuɗaɗe ne da ake neman su yi bayani a kai.

PREMIUM TIMES ta gano wasu bayanai na yadda aka rika jibga kudɗade masu yawa a wasu asusun bankuna na kamfanini mallakin tsohon gwamnan.

Misali akwai asusun da aka saka naira miliyan 200 cinkin kwana ɗaya sannan washe gari aka ci gaba da jibga kuɗade a wannan asusun banki duk wanda aka gano kuɗaɗen cin hanci ne da ƴan kwangila ke maido wa gwamnan kason sa na harƙallar.

An gano wasu kamfanoni mallakin gwamnan da matarsa har 55 da aka rika jibgawa a asusun bankunan waɗannan kamfanoni kuɗade babu ƙaƙƙauta a tsawon mulkin sa a Nasarawa shekara 8.

An gano asusun banki na wani kamfanin sa da kafin ya zama gwamna dala 250 kacal ke cikin asusun, amma tun bayan zaman sa gwamna, sai aka rika jibga kuɗaɗe a wannan asusu, shiga kawai suke yi suna fita ana harƙallar su.

Daya daga cikin kamfanonin sa da ya shahara wajen shige da ficen ƙudade akai-akai shine Otel din sa mai suna Ta’al da wasu Kamfanoni.

Share.

game da Author