Siyasar Jihar Zamfara tana cigaba da daukar sabon salo tun bayan chanza shekar da gwamna Bello Matawalle yayi daga Jam’iyyar PDP zuwa APC hakan ya janyo an fara ganin chanjin sheka daga Yan siyasar Jihar.
Imran Ahmad-Rufa’i shi ne maitemakawa tsohon dan takarar gwamna, Muktar Idris, a karkashin Jam’iyyar APC ya ajiya mukaminsa, yace bayayi amma bai furta inda ya kuma ba.
Ahmad-Rufa’i yace ya yanke shawarar hakan ne bayan yayi shawara mai zurfi da abokan siyasarsa kuma yayiwa tsohon maigidansa fatan alkhairi.
Ya kuma cewa, “a duk tsawon shekarun da nayi, Allah ya bani dama na haduwa da muhimman mutane wadanda suka canza rayuwata ta fannoni da dama, wanda yayi fice shine Hon. Mukhtar Shehu Idris (Kogunan Gusau).
Na sami damar yin aiki tare da Koguna a cikin shekaru 4 da suka gabata kan lamuran siyasa da na sirri, duk da cewa ba da takamemmen mukami ba. Wannan abun alfahari ne da daukaka yin aiki ga irin wannan fitaccen mutum mai dinbin halaye da dabi’u masu kyau, inji Ahmad-Rufa’i.
“A wannan rana nabar wakiltar Idris a kafafen yada labarai a ko wani dandali. Wannan ya kasance hukunci mai nauyi amma mai muhimmanci a wurina.
“Tare da ban girma, Ina godiya ga Koguna akan wannan dama mai muhimmanci da ya bani, ina godiya ga duk danginsa da abokansa dana mu’amalanta a lokacin tarayya ta dashi, inji Ahmad-Rufa’i.
Muktar dris yayi takarar gwamna a 2019 a karkashin Jam’iyyar APC hukumar INEC ta sanar cewa ya lashe zabe amma daga baya kotun koli ta sauke zaben saboda rashin yin zaben cikin gida.