RIGERIGEN SHIGA APC: Sakataren APGA, Sanatan Zamfara da Ƴan majalisan Tarayya biyu sun canja sheka zuwa APC

0

Tsohon sakataren Jam’iyyar APGA na kasa Sani Shinkafi ya koma jam’iyyar APC bayan shekaru 19 da yayi a jam’iyyar APGA.

Shinkafi ya bayyana cewa da kansa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bukaci ya koma jam’iyyar APC tare da shi, a yau Talata.

” Na koma APC tare da duka ƴan jam’iyyar APGA kaf ɗin su dake ke kananan hukumomi 14 na jihar Zamfara.

Haka kuma a majalisar Tarayya ranar Talata, kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ya sanar a zauren majalisar cewa ƴan majalisa Lego Idagbo, dake wakiltar Beckwara/Obudu/Obanliku da Michael Etaba dake wakiltar Obubra/ Etung, jihar Koross Ribas duk sun fice daga PDP sun koma jam’iyyar APC.

Har yanzu dai daga jihar Zamfara, Sanata Hassan Gusau ya canja sheka zuwa APC daga PDP.

Sanata Hassan Gusau na daga cikin wadanda suka samu kujerar tsinci kujerar sanata daga sama gasassa domin a dalilin hukuncin kotun ƙoli da ya soke zabukan APC gana ɗaya ya bai wa PDP ya sa suke bisa kujeru yanzu.

Share.

game da Author