Masu shakar hayakin sigari ba su tsira ba, mutum miliyan 1.2 na mutuwa duk shekara a Afirka – Inji WHO

0

Shugabar kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO na yankin Afrika Matshidiso Moeti ta bayyana cewe sakamakon bincike ya nuna cewa mutum miliyan 1.2 ne ke mutuwa a dalilin shakar hayakin taba sigari duk shekara a nahiyar Afrika.

Matshidiso ta fadi haka ne a ranar taba sigari ta duniya da ake yi ranar 31 ga watan Mayu na kowacce shekara.

Taken ranar na bana shine ‘Mai da hankali wajen guje wa busa taba sigari’.

Taba sigari na hadassa cutar dajin dake kama baki, makogwaro, huhu, ciwon siga da sauran su.

Mutum na iya kamuwa da wadannan matsaloli koda ko karan sigari daya yake busawa lokaci-lokaci ko Kuma yana shakan hayakin ba tare da yana busa sigarin ba.

“A lokacin da cutar korona ta bullo WHO ta yi nasarar karkato da ra’ayoyin mutane suka daina shan taba a Afirka.

Matshidiso ta ce a lokacin da korona ta bullo mutum biliyan 1.3 ne ke busa taba sigari a duniya inda daga ciki kashi 60% suka daina sha.

Matshidiso ta ce a kasashen Angola, Botswana, Zambia da wasu kasashen Afrika 11 ana bai wa mutanen dake son daina shan taba sigari shawarar yadda za su yi kyauta a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.

Wasu kasashen Afrika guda shiga sun bada lambobin wayar salula da mutane za su kira idan suna bukatar daina shan taba sigari.

Share.

game da Author