RASHIN TSARO: ‘Yan Kasuwa da masu cin Kasuwa sun kaurace wa Kasuwar Duniya ta Kaduna

0

Duk wanda ya san yadda Kasuwar Duniya ta Kaduna ke ci a shekarun baya, zai zauna ya rika sharba kuka idan ya ziyarci dandalin Kasuwar da ke ci a yanzu haka dake titin Kaduna zuwa Zariya saboda karancin ‘yan kasuwa da masu cin kasuwa bana.

Ana yi mata Take da Kasuwar duniya ta Kaduna da ta fi kowacce Kasuwa da ake ci dyuk shekara a nahiyar Afirka.

Wasu abubuwan idan ka gansu a kasuwar sai kuma wata shekarar, ba za ka kara ganin su ba.

Amma kuma a wannan shekara ba irin haka za ka iske ba idan ka ziyarci kasuwar da ke ci na bana.

Masu ci da ‘yan kasuwan dake ci a karo na 42 sai su baka tausayi, kusan kasuwar unguwa ta fita tasiri.

A bukin bude kasuwar baje kolin ranar Juma’a amma zuwa ranar Lahadi mutane da ‘yan kasuwa kalilan ne ke shawagi a kasuwar.

Wasu ‘yan kasuwa da suka baje koli su a kasuwar sun bayyana cewa bana zai yi wuya ‘yan kasuwa su samu abinda suke so saboda rashin zuwan mutane kasuwa.

Mataimakin manajan kamfanin Springfield Agro Ltd., Musa Usman ya koka kan rashin zuwan masu cin kasuwa dandalin.

Manajan kamfanin Tech Africa Nigeria Ltd., dake Abuja Ibrahim Mohammed ya ce akwai yiwuwar saboda korona ne mutane suka ki fitowa amma yana sa ran kila mutane za garzayo nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.

Babban abinda ya sa mutane ke fargabar fitowa yanzu bai wuce matsalar rashin tsaro da ba da ake fama da shi a kasar nan. Wasu daga cikin wadanda aka tattauna da su sun bayyana cewa akwai yiwuwar kasuwar zata dan cika kafin ranar rufe ta ya zagayo, wato 6 ga watan Yuni.

Share.

game da Author