Zargi: Wani bidiyo mai dauke da gawawwakin sojoji na daukar hankalin jama’a bisa zargin cewa dakarun Najeriya ne wadanda kungiyar Boko Haram ta hallaka kwanan-nan
Gwagwarmayar Najeriya da matsalar hare-hare na daya daga cikin manyan rikice-rikicen yankin yammacin Afirka. Kuma badun irin yunkurin da dakarun sojojin Najeriyar ke yi dan dakile masu kai harin, hare-haren sun cigaba da ta’azara, abun da har ya sanya milliyoyin mutane rasa matsugunnensu a yayinda wasu dubu 30 kuma suka rasa rayukansu a yankin arewacin Najeriya, ciki har da jami’an tsaron kansu.
Ba da dadewa ba kungiyar Boko Haram da wasu kungiyoyin masu kaifin kishin addini suka farfado da ayyukansu suka kuma kara yawan irin hare-haren da sukan kai kan jami’an tsaron Najeriyar. Kusan sojoji 30 suka hallaka a watan Afrilu a wasu hare-hare 4, wadanda kungiyoyin masu kishin addinin suka kai a yankin arewa maso gabashin Najeriyar, a cewar wani rahoto. Har ila yau a wannan yankin, ‘yan ta’addan sun kai hari kan wani ofishin ‘yan sanda a Damasak da ke jihar Borno.
Wani hoton bidiyon da aka yada sau da yawa a manhajan whatsapp ya nuna gawawwakin sojoji da harsasai suka yi kaca-kaca da su. Wannan bidiyon wanda whatsapp ta ce an yada shi ya fi a irga an yi mi shi taken “Boko Haram yayin da suke kashe dakaru Najeriya,” abun da ke nufin cewa sojojin Najeriya aka raunata a daya daga cikin hare-haren bayan nan da kungiyar Boko Haram ta kai.
A bidiyon mai tsawon mintuna 4:29, an jiyo ‘yan ta’addan suna cewa “Allahu Akbar” yayin da suke kwashe bindigogi, riguna masu sulke da harsasan sojojin da suka hallaka. Hotunan bidiyon ba su yi kyau sosai ba, kuma a wasu hotunan ba’a gane abin da ke ciki da kyau abin da ke nuna cewa karfin kaifin hotunan bidiyon ya ragu sosai saboda tsananin yawan yada shi da aka yi a shafukan sada zumunta.
Dubawa ta kuma gano cewa wani Anderson Micar, mai amfani da shafin twitter ya wallafa takaitaccen bidiyon wanda bai kai minti hudu ba, tare da taken “Boko Haram na kashe sojojin Najeriya kamar kaji. Wai shin wane irin makamai dakarun Najeriya ke amfani da su wajen yakarsu. Watakila duwatsu da sanduna.”
TANTANCEWA
Dubawa ta fara da nazarin bidiyon a manhajar VLC wanda akan yi amfani da ita wajen kallon bidiyo, daga nan ta yi amfani da sigma wanda ke inganta hotunan bidiyo tunda hotonan basu fita da kyau ba. Mun kuma yi amfani da abun da ke sa hotunan bidiyon su yi tafiya a hankali domin mu iya daukar hotuna.
Bayan da muka yi amfani da wadannan kayayyakin muka inganta hotunan cikin bidiyon, DUBAWA ta gano cewa lambobin da ke kan motocin dakarun sojin na dauke da tutar kasar Mali, wanda ke da kaloli uku – wato kore, ruwan kwai da ja. Wannan ya tabbatar mana da cewa motocin da gawawwakin duk na dakarun Mali ne. Lambobi biyu da muka tantance cikin bidiyon sun hada da 010680 AMA da 010676 AMA.
DUBAWA ta kuma kara da wani binciken a manhajan tantance hotuna na Yandex, inda ta yi amfani da daya daga cikin hotunan da ta dauka a cikin bidiyon. A nan ne ta gano motocin sojojin Mali na da kamanni sosai da wadanda ke cikin bidiyon, (dan tabbatar da hakan ta yi amfani da Lambar motar, da kalar rigar yakin sojoji) suna kuma kama da motocin da aka yi amfani da su lokacin juyin mulkin Mali a shekara ta 2020.
Bugu da kari, binciken kalmomi ya kuma nuna cewa lallai motocin na dakarun Mali ne wadanda aka fi sani da FAMA wato Forces Armées Maliennes.
DUBAWA ta kuma gano cewa wani launin kalolin sojoji na daban ne dakarun Najeriya da motocinsu ke amfani da shi, kuma wannan wani launin wanda aka fi gani a rigunan yakin sojojin ya banbanta daga na dakarun Mali da ma na sauran sojojin kasashen Afirka.
Haka nan kuma binciken ya sake gano cewa kungiyar da ta kai harin da ya yi sanadin hallakar wadannan sojojin ba za ta iya kasancewa Boko Haram ba domin ita Boko Haram ba ta aiki a Mali. Maharan cikin bidiyon watakila mambobin kungiyar Jama’at Nusrat Islam wal Muslimeen (JNIM), ko kuma ta Islamic State Greater Sahara (ISGS) ko kuma irin kungiyoyin ta’addan da ke aiki a kasashen da ke amfani da harshen faransanci.
A Karshe
Bidiyon da ke ikirarin cewa Boko Haram suka kashe sojojin Najeriya karya ne. Sojojin da ke cikin bidiyon ba dakarun Najeriya ba ne kuma mawannan kisa ba a Najeriya ya faru ba.