‘Barka da zuwa Matawalle, In ji Bashir Ahmad, ‘Matawalle bai koma APC ba, In ji Kakakinsa

0

Duk da rubuta taya murna da yin maraba da dawowa APC da hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmed yayi wa gwamnan Zamfara, Bello Matawwlle, a shafin sa ta Facebook, Kakakin Matawalle Yusuf Bello, ya karyata haka.

Wannan ba shine karon farko da Matawalle ke ja wa APC rai ba. An daɗe ana ga shanunan amma shiru.

Sai dai kuma da yake wannan karon hadimin shugaba Buhari ne ya rubuta a shafinsa na Facebook, sai abin yayi tasiri.

Bashir Ahmad, ya rubuta ” Toh, ya tabbata Zamfara ta dawo gida, Barka da zuwa Matawalle”.

Sai dai kuma duk da saka wannan sako da Bashir yayi, Kakakin gwamna Matawalle ya karyata maganar, ya ce gwamnan bai koma APC ba.

Wasu daga cikin makusantan gwamnan sun shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa lallai akwai maganar canja sheka da Matawalle zai yi. Sun bayyana cewa tuni har an fara musanya tutucin PDP zuwa APC a jihar.

Idan Matawalle ya koma APC, zai zamo gwamnan PDP na biyu kenan da ya koma APC a cikin watanni biyu.

Idan ba a manta ba, ba wannan bane karon farko da ake yada cewa Matawalle zai koma APC ba, hatta wasu daga cikin makarraban sa duk sun taba tabbatar da haka amma kuma daga baya ya fito ya karyata su.

Amma kuma sai dai idan aka lura, za a ga Matawalle ba ya halartar tarukan jam’iyyar PDP. A taron bayabayan nan da aka yi ma, mataimakin sa ne ya halarci wannan taro.

Share.

game da Author