Sai fa Najeriya ta daina biyan tallafin man fetur za ta iya ci gaba – Ministan Mai

0

Ƙaramin Ministan Harkokin Man Fetur, Timipre Sylva ya bayyana cewa Najeriya za ta ci gaba tuma tsalle wuri ɗaya ta na gumi, maimakon ta yi gudu wajen ci gaba matsawar Gwamnatin Tarayya ba ta daina biyan tallafin man fetur ba.

Ya ce idan aka janye tallafin man fetur, to a haka sai fetur ya sayar da kan sa a kasuwa daidai da darajar sa, wadda inji ministan, ta haka ne tallalin arzikin Najeriya zai bunƙasa.

Sylva ya yi wannan kintace ne a wata tattaunawar sanin mafita da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ranar Lahadi, a Abuja.

“Ni dama matsayi na a kan bayan tallafin mai da gwamnati ke yi, a bayyane ya ke. Na yi amanna cewa idan har ana so arziki da tattalin Najeriya su bunƙasa, to tilas sai an cire tattalin mai, yadda za a bar fetur ya yi wa kan sa daraja da kan sa a kasuwanni.

Gwamnati Ta Gaji Da Sayar Da Fetur Arha Takyaf -Ministan Fetur

Karamin Ministan Fetur, Timipre Sylva ya bayyana cewa, “Ba abin alheri ba ne ga gwamnati a ce ta na haƙo fetur a farashi mai tsada, sannan ya riƙa sayar da shi arha takyaf ga jama’a, don kawai ta sauƙaƙe masu wani nauyi a kan su.

“Abu ne da za a so a riƙa yi kam. Amma kuma ba abu ne mai ɗorewa ba. Saboda bai yiwuwa ka haƙo abu a misali kan naira 10, sannan ka riƙa sayarwa naira 5 a kullum.

“Ba ya asarar da ka ke ɗibgawa, hakan na nufin duk lokacin da za a sake haƙo shi, sai ka ci gaba da ƙara naira biyar ɗin da ka rage kenan.

“A kullum asarar ka tun ta na ƙara yawa, har ta koma a kullum ta na ninkawa. To irin wannan gagarimar asara ce ta kawo mu cikin mawuyacin halin da mu ke cikin yanzu.”

Ya ce wasu mutane na ganin cewa idan aka gyara matattun mai kamar za a magance shigo da tataccen fetur cikin ƙasar nan.

Ya ce ai kuɗin tallafin mai da ake biya su ne musabbabin da matatun mai na ƙasar nan su ka daina aiki.

Share.

game da Author