Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko, NPHCDA ta bayyana cewa mutum miliyan 2,099,568 ne suka yi allurar rigakafin cutar korona da ruwan maganin Oxford/AstraZeneca a zangon farko a kasar nan.
Shugaban hukumar Faisal Shu’aib ya sanar da haka a taron da ya yi da manema labarai a Abuja a karshen makon jiya.
Shu’aib ya ce zuwa yanzu mutum miliyan 1,005,234 ne suka yi allurar rigakafin cutar a zango na biyu a kasar nan.
Ya kuma ce gwamnati ta kara yawan kwanakin da za a yi domin yi wa mutane allurar rigakafin daga ranar 25 ga Yuni zuwa ranar 5 ga Yuli.
Shu’aib ya yi kira ga wadanda suka yi allurar rigakafin zangon farko kafin ranar 13 ga Mayu da su hanzarta zuwa wuraren yin allurar rigakafin mafi kusa da su domin su yi allurar zango na biyu.
Ya kara kira ga ‘yan Najeriya musamman wadanda basu yi allurar rigakafin ba da su gaggauta yin allurar domin har yanzu ana yi wa mutane allurar a kasar nan.
Bayan haka Shu’aib ya gargaɗi mutane da su ci gaba da kiyaye sharuɗɗan gujewa kamuwa da cutar ko da kuwa sun yi allurar rigakafin.
Ya ce yin haka zai tabbatar da hana yaduwar cutar.
Shu’aib ya ce bayan an yi amfani da miliyan uku na kwalaben maganin rigakafin an samu rahotanin cewa mutum 13,267 sun fuskanci matsala bayan an yi musu allurar rigakafin.
Ya gargaɗi mutane da su kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin cutar ta sake barkewa karo na uku a wasu kasashen Afrika.
Discussion about this post