Yin aiki fiye da awa 55 a mako daya ya yi sanadiyyar rayukan mutum 745,000 a duniya – WHO da ILO

0

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO da kungiyar kwadago ta ƙasa da kasa ILO sun bayyana cewa yin aiki sama da awa 55 a mako ya yi ajalin mutum 745,000 a duniya a cikin shekarar 2016.

Kungiyoyin sun ce wani sakamakon bincike da suka gudanar a kasashe 154 daga shekarar 1970 zuwa 2018 ya bayyana haka.

Bisa ga sakamakon binciken a shekarar 2016 mutum 398, 000 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar shanyewar bangaren jiki sannan mutum 347, 000 sun mutu a dalilin kamuwa da cututtukan dake kama zuciya.

Hakan ya auku ne a dalilin yawaita yin aiki sama da awa 55 a mako.

Sakamakon ya kuma nuna cewa yawan mutanen dake mutuwa a dalilin kamuwa da cututtukan dake kama zuciya ya karu daga Kashi 19% zuwa kashi 42% a duniya daga shekarun 2000 zuwa 2016.

Binciken ya nuna cewa matsaloli irin haka ya fi afka wa maza masu shekaru daga 45 zuwa 74.

A takaice dai WHO ta ce yawaita yin aiki sama da awa 55 a mako na hadassa kashi 35% na cutar shanyewar sashen jiki da kashi 17% na cututtukan dake kama zuciya fiye da idan mutum ya yi aiki awa 35 zuwa 40 a mako.

Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya yi kira ga gwamnatocin kasashen duniya da su kafa dokokin da za su taimaka wajen hana mutane yin aiki sama da awa 55 a mako.

Ya kuma yi kira ga ma’aikata da su rika raba yawan awowin da ya kamata su yi aiki a mako a tsakanin su ma’aikata domin kare kiwon lafiyar su.

Wannan shine karon farko da aka gudanar da bincike kan yadda yawan aiki ke cutar da lafiyar mutane a duniya.

Share.

game da Author