A ranar Talata ce jirgin sama na kamfanin Max Air dauke da Sarkin Kano Aminu Ado-Bayaro, ya yi saukar gaggawa, minti 10 kacal bayan tashin sa daga filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA).
Jirgin mai lamba VM1645, ya na dauke da fasinjoji da dama baya ga Sarkin Kano a ciki. An shirya jirgin zai tashi da karfe 1:30 na rana, amma aka samu jinkiri na mintina 30.
An ruwaito cewa minti 10 bayan jirgin ya cira sama, ya fara tangal-tangal, amma ya samu nasarar juyawa baya, ya koma filin jirgin Kano ya sauka.
Sai dai kuma Daraktan Kula da Lafiyar Jirage na Max Air, Muhammad Mubaraq ya karyata rahotannin da wasu jaridu su ka ce injin jirgin ne ya samu matsala a sama. Kuma ya ce karya ce, babu wanda ya kusa mutuwa a cikin jirgin.
“Tsuntsaye ne aka samu akasi su ka kutsa cikin injin jirgin. Kuma wannan ba wani abin tayar da hankali ba ne, domin matukin jirgin ya bi ka’idojin da aka shimfida. Wato idan haka ta faru, ya koma inda ya fito idan ya fi masa kusa.” Inji Mubaraq.
“Yanzu haka jirgin tuni an gama duba lafiyar sa, har ya tafi Abuja daga Kano. Saboda haka ba daidai ba ne a rika cewa jirgin ya kusa rikitowa ya kashe mutanen da ke cikin sa.
“Kuma su tsuntsaye ai sun saba yi wa jirage cikas bayan jiragen sun tashi sama.”