Jami’an tsaro sun kwato shannu 300 da aka sace ciki dare daya a jihar.
Gwamnan jihar Bello Matawalle ya sanar da haka a liyafar bude bakin da ya yi da manema labarai a fadar gwamnati ranar Lahadi.
“Mun samu labarin cewa wasu barayin shanu sun sace shannu a kauyen Kuraji, nan da nan muka aika da jami’an tsaro wannan gari domin dakile su.
“Ganin jami’an taron sai barayin suka gudu suka bar shanun.
Ya ce shanu na wajen jami’an tsaro kuma nan ba da dadewa ba gwamnati za ta fitar da sanarwa domin wadanda aka sace wa shanun su zo su karbi dabobin su.
Matawalle ya ce kauyen Kuraji na daya daga cikin wurare a jihar da ya zama masaukin mahara da masu garkuwa da mutane. Ya kara da cewa gwamnati ba za ta yi kasa-kasa ba wajen hukunta wanda aka kama da hannu a ayyukan ta’addanci a jihar.
Ya yi kira ga mutane da su ci gaba da ba baiwa jami’an tsaro hadin kai domina kawo karshen hare-haren da garkuwa da mutane da ya addabi mutanen jihar.
A ranar 20 ga Afrilu PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda dakarun ‘yan sandan jihar Katsina suka kashe wasu mahara uku kuma suka kwato dabobbi 330 a jihar.
‘Yan sandan sun yi arangama da maharan a Mararabar-Gurbi inda suka kwato babban bindiga AK47 guda daya, shannu 160, tumaki 170 da babura biyu.
Discussion about this post