Wani matashi mai shekaru 19 mai suna Ibrahim Kabiru dake yankan farce a garin Benin jihar Edo ya bayyana cewa duk wata yana cinikin naira 45,000 a sana’ar da yake yi.
A tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, Kabiru ya ce ya zo ci rani daga kauyen sa a jihar Sokoto zuwa jihar Edo domin yin sana’ar yankan farce.
Ya ce a da noman masara yake yi amma rashin kudi ya hana shi ci gaba da noman.
Kabiru ya ce ya kashe naira 1000 wajen siyan almakashi, abin yanke kumba, soso da sabulu kuma a duk rana yana samun naira 1,500.
“Ina karban Naira 50 a yankan farce hannu ko kafa, naira 100 a yankan farcen kafa da hannu.
Ya ce yana alfahari da sana’arsa domin dalilin sana’ar sa yake biya wa kansa da iyalinsa bukatu.
Kabiru ya ce matsalarsa da sana’ar shine yadda yake yawo lungu-lungu, kwararo-kwararo domin yanke wa mutane kumba.
Duk da haka ya ce gwanda sana’ar da zaman banza a gida.
Kabiru ya ce zai iya komawa gida domin ci gaba da noma idan har zai samu tallafi.
Ya ce bashi da ilimin boko amma yana dogara da noman masara da sana’ar yankan farce domin ciyar da kansa da iyalinsa.
Discussion about this post