KISAN RUBDUGU A BAUCHI: Gwamnatin Jiha ta kashe kaji 27,000 don hana cutar murar tsuntsaye bazuwa

0

Gwamnatin Jihar Bauchi ta bada sanarwar kashe kajin gidan gona har guda 27,000, domin hana cutar murar tsuntsaye yaduwa.

Shugaban Kwamitin Hana Cutar Murar Tsuntsaye Bazuwa na Jihar Bauchi, Samaila Burga ne ys bayyana haka ranar Juma’a a Bauchi. Ya ce gidan kiwon kaji 9 ne ciwon ya bulla a cikin kananan hukumomi biyu.

Kananan Hukumomin biyu sun hada da Bauchi da kuma Toro.

“An kashe kaji 27,000 a wani gidan kaji daya da ke cikin kananan hukumomin biyu, domin a hana cutar fantsama cikin sauran kananan hukumomin jihar.

Burga ya ce Kwamishinan Ayyukan Noma da Raya Karkara na Jihar Bauchi ne ya kafa kwamitin.

“Kuma Kwamishinan Ayyukan Gona da Raya Karkara na Jihar Bauchi ya karkasa likitocin dabbobi har su 130 zuwa kananan hukumomin jihar guda 20, domin sa-ido kan yiwuwar bullar cutar da kuma saurin dakile inda ta bulla fadin jihar Bauchi.

Ya ce za a ci gaba da wayar wa jama’a kai, musamman masu kiwon kaji.

Yayin da ya ke gargadin masu mu’amala da kaji su rika kiyayewa da ka’idojin da aka shimfida.

A karshe ya kara gargadin jama’a cewa a guji cin kajin da ake kyautata zaton sun kamu da cutar murar tsuntsaye.

Share.

game da Author