Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
‘Yan uwa masu daraja, kamar yadda kuka sani ne, kuma kamar yadda muka bayyana maku ne, kuma alhamdulillah, kuka amince da bayanan mu, domin kuna sane da cewa, ba zamu yi maku karya ba, kuma ba zamu yaudare ku ba. Muna gode maku kwarai akan wannan.
Makiya, makirai, magauta, shedanu, jahilai, wawaye, sun yada wani hoto tare da bayanin karya, da sharri, da kazafi, da nufin su bata sunan Mai Martaba, Khalifah, Sarki Malam Muhammadu Sanusi II, saboda suna bakin ciki, da jin haushin irin baiwar da Allah yayi masa ta dimbin mabiya da masoya a cikin fadin duniya, to amma da yake Allah ba azzalumi bane, baya zalunci, kuma ya hana zalunci, sai ya tona asirin su, ya tozarta su, suka kunyata!
Gaskiyar magana ita ce, Khalifah ya jagoranci Sallah kamar yadda aka saba, bayan idar da Sallah, sai ya mike domin ya tarbi wasu baki da suka kawo masa ziyara, daga nan kuma sai yaci gaba da karantar da al’ummah lamarin addinin su, kamar yadda kowa yasan cewa, wannan daya ne daga cikin ayukkan da ya saka a gaba, wato kokarin fahimtar da al’ummah su fahimci duniyar su da lahirar su, fahimta ta gaskiya.
A lokacin idar da Sallar, sai Sarki ya mike tsaye, ya bar wasu masbukai, wadanda suka bi shi Sallah daga baya, suna cika Sallar da ta rage masu. Faruwar wannan lamari, kawai kwatsam, sai makiya Allah da Manzon sa (SAW), suka juya manufar wannan hoto, suka canza gaskiyar lamari, suka tafi suna posting a social media, wai cewa wadannan mutane, suna yin sujadah ce, irin wadda ake yiwa Allah Ta’ala, ga Sarki Muhammadu Sanusi II. Subhanallah! Subhanallah!! Subhanallah!!!
Wanda alhamdulillahi, suna fadar wannan karya, sai Allah ya tona masu asiri, al’ummah suka yi caa akan su, aka fara la’anta da tsinuwa akan su.
Jama’ah suka tabbatar, da kan su, cewa wallahi wannan zance karya ne, domin yadda suka san Mai Martaba, Khalifah, Sarki Malam Muhammadu Sanusi II, sun yi imani da Allah, ba zai yi wannan ba, kuma ba zai taba yadda ayi masa sujadah ba!
Saboda haka Jama’ah, kun ga yadda Allah yake gudanar da al’amarin sa, duk lokacin da wasu makirai suka hura wutar yaki, sai Allah ya kashe ta, da karfin ikon sa, da iyawar sa; ba da iyawar mu ba, sannan ba da wayon mu ba.
Kai ko hasidin iza hasada ya san Sarki Muhammadu Sanusi II ba jahili bane, kuma sam ba zai yadda da aikin jahilci da jahilai ba!
Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun! Ta yaya Mai Martaba zai yarda ayi masa sujadah? Wallahi sam, ba zai taba yiwuwa ba!
Ya ku al’ummah, wannan sakon karin bayani ne, tare da kara jaddada godiyar mu ga al’ummah, da suka kyautata wa Khalifah zato akan wannan lamari.
Mungode, mungode, mungode.
Muna rokon Allah ya bar kauna da soyayya, amin.
Wassalamu Alaikum
Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, 08038289761. Lahadi, 16/05/2021.